Da na tuna masa cewa ranka ya dade na san ka fi kowa sanin jama’ar Arewa su ne suka fi kowa nuna maka soyayya tare da yi maka ruwan kuru’u a zabe na farko wanda ya kawo ka a matsayin Shugaban kasa na wa’adin da ya gabata da kuma zaben da aka sake yi a wannan shekarar wanda ya baka damar sake darewa akan karagar mulki a karo na biyu, har yanzu jama’a da dama ciki har da Mai dakinka suna da ra’ayin cewa yankin na Arewa shi ne kutal wajen amfana da muhimman ayyukan da gwamnatin ka ta gabatar a zangonka na farko. Akwai uzuri da yawa da jama’ar wannan yanki suka yi ma dangane da ganin yadda ake zargin wasu yan majalisa na tarayya da yi ma gwamnatinka tarnaki saboda wasu muradu na kansu da kuma lalurar rashin lafiya da ta faru da kai a cikin wa’adin na farko, har ta kai ana ’yan’adawa na maka lakabi da Dan Amarya ba ka laifi.
Da farko jama’ar Arewacin kasar nan na da abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya wadanda kuma suke ganin har yanzu ba ka yi masu abin da suke tsammani ba. misali wutar lantarki a Arewa wannan za a ce fa ana nan jiya I yau. Har yanzu ana dauke wuta sau da yawa a kowace rana ta duniya sannan ga tsadar kudin da ake caji jama’a a karshen wata karuwa ya yi ba raguwa ya yi ba. Uwa uba kuma ga yadda Kamfanonan da ke samar da wutar suka gaza wajen samar da Mitocin wuta na zamani kamar yadda suka alkawalta. Wannan kuwa tarnaki ne ga habakar tattalin arziki da kuma rage zaman kashe wando.
Idan ka dauki maganar tsaro tilas a yaba maka a yankin Arewa maso Gabas amma kuma a gaskiya tilas a ce ka yi sake mai yawa ta yadda ka bar matsalar makiyaya da Manoma a yankin Arewa maso yamma ta girma ta rikide ta koma taáddanci da yin garkuwa da jama’a inda a kullum ake ta lakume rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da kuma asarar dukiya mai yawa.
Akwai zarge zarge na cewa a mafiya yawan shirye shirye da aka gabatar don rage radadin talauci da kuma samar da ayyukan yi ga matasa na kasa an yi ma Arewa mi’ara koma baya ta yadda a zahiri ba a alkalumma ba mai Doki ya koma kan kuturi. Domin kuwa mutanen wannan yanki na fama da tsananin talauci, ga rashin aikin yi a tsakanin matasan wannan yanki. Ko da wajen daukar ma’aikata ma ana yi ma Arewa ýar burum burum ta hanyar shelantawa tallar ayyukan a yanar gizo amma daga bisani in baka da kudi sai dai jirgi ya bar ka a tasha.
Haka kuma abin yake ga sauran manyan ayyuka da aka gabatar a cikin kasa na gina manyan tituna da Jami’o’i. A batun aikin yashe Teku na Baro kuwa sai dan makullin gishiri yak enema ya fi gishirin zaki sannan kuma ayyukan samar da tashoshin sabke kaya doron kasa a gaskiya duk aikin ya fi yawa a takarda. Yaki da cin hanci da rashawa kuma ya koma sai ga ’ya’yan mora amma mai uwa a murhu kuwa ko da an dauko batunsa rigi-rigi to sai da a ji sakwab. Daga nan kuma sai dai ka ji shiru wai Malam ya ci Shirwa.
Maganar Layukan Dogo kuwa da ake ginawa har yau na gefen Arewa a takarda suke, ba a saukar da su a kasa ba. Ga Masana’antu birjik a Kano da Katsina da Kaduna da Gusau da Lakwaja da sauran garuruwa na Arewa na saka tufafi da na sarrafa tama da karafa da na jima da kira da na sarrafa kayan gona da suka mutu da a da ake sanya ran za ka farfado da su cikin sauri tun a hawanka na farko amma har shekaru hudu ta shude ba wacce ta motsa.
Don haka a wannan zagaye na biyu mutanen wannan yanki na cike da tsammani da kyakkyawar fata na ganin ka yi tozali da barkono wajen hukunta duk masu hannu a ayyukan cin hanci da rashawa da kuma ayyukan ta’addanci don kawo karshe wadannan matsaloli da suka zamo annoba. Sannan kuma ka inganta hanyoyin noma wajen samar da Kamfanonin da za su rinka sarrafa wasu abubuwa da muke da su kamar shara ta bola da kuma ta gona don rinka samar da takin zamani a cikin gida ta yadda Takin zai zama kamar gyada gasassa.
Haka kuma ya kamata gwamnatin Tarayya da na Jihohin Arewa su hada hannu su sawo motocin noma da kayan aikinsu na zamani masu yawa wadanda Manoma za su iya dauka haya cikin farashi mai sauki su yi masu aiki a gonakinsu don rubanya abin da ake samarwa na daga albarkatun noma. Mafiya yawan madatsun ruwa da Dam da ake da su a garuruwan Arewa sun cike wasu ma babu su kuma muna sanya idanu mu ga ka sake gina su domin bayan noman rani da kuma samar da ruwan sha ga jama’a da dabbobi da kuma samar da kifi akwai ayyukansu da gudunmawarsu ga jama’a ba ma za su misaltu ba.
Da can mun yi zaton da ka hau magani zai wadatu a asibitoci cikin farashi mai sauki kamar yadda ka yi lokaci kana PTF, amma ga shi yanzu babu fanado a kasa. Haka kuma muka yi ta tunani z aka dinga tsaga hanyoyi ana gina su mul-mul-mul kamar zamanin PTF sai har kawo yanzu ko hanyar Kano zuwa Abuja ba ta kamala ba.
Sannan kuma karin albashin da gwamnatinka ta amince da shi ya kamata a ce an yi irin abun nan wato da aka ce ma Kare ana buki a gidansu shi kuwa sai ya ce in gani a kasa. Dumbin jama’ar kasa ciki har da na jama’ar Arewa sun sake zabarka ne saboda suna maka kyakkyawan zato na z aka iya kara ma Malaman makaranta da Jami’an tsaro albashi wanda a kalla ko bai fi na Kansila ba ya zo daidai da shi. Don kuwa yin haka shi ne zai daidaita tazarar da take a tsakanin masu rike mukaman siyasa da kuma ainihin maáikatan gwamnati wanda hakan yana nufin rage cin hanci da rashawa da kuma inganta ayyukan Malaman Makarantu.
Batun filayen saukar Jiragen sama da muke da su a Arewa kamar na Kano da Kaduna da ya kamata a ce tunda namu ya kama an daga darajarsu bisa cancanta sun kai tsara wajen matsayi da kayan aiki na zamani, don inganta harkokin kasuwanci da yawon bude ido amma ga shi sai dai a ce wata miyar sai dai a makwabta. Don haka ya kamata ta canja zane domin da zafi-zafi kan bugi karfe. Tun kafin hadarin siyasar ya debo wata dambarwar mai sarkakiya gara Baba ka tuna cewa fa idan ma har ba a yi kwado da yaro to gara a bashi dan gayansa, don gudun ka da a gama yaki a bar Arewa da kuturun bawa.
Iro ya aiko ra’ayin nan daga Abuja
0816 343 9197