✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da sana’ar walda na yi aure, na mallaki gidan kaina -Kabiru Gurgu

Kabiru Sabo, magidanci ne mai kimanin shekaru 35, wanda kuma gurgu ne. Duk da nakasar da yake da ita, ba ta hana shi neman na…

Kabiru Sabo, magidanci ne mai kimanin shekaru 35, wanda kuma gurgu ne. Duk da nakasar da yake da ita, ba ta hana shi neman na kansa ba, domin a yanzu haka shi fitaccen mai sana’ar walda ne a Jihar Kano.
Kabiru Sabo, wanda ke da mata daya da ’ya’ya biyar, ya bayyana wa Aminiya cewa nakasar rashin kafa ta same shi ne, yayin da katangar dakin da suke kwana ta zama sanadi tun yana dan shekara goma da haihuwa. “Wata rana cikin damina muna kwance a daki, ni da wasu ’yan uwana biyu, sai katangar dakin ta fado mana. A nan daya daga cikinmu ya rasu, dayan kuma babu abin da ya same shi, a yanzu haka ma yana nan yana gudanar da sana’ar gini. Sai ni kuma da na sami karaya a kafata, daga baya kafar ta lalace aka yanke ta. Sai dai duk da haka ban daina zuwa makaranta ba, domin a lokacin ina aji hudu a firamaren Gandun Albasa. A wannan hali na ci gaba da karatuna har na kammala firmare da sakandare ina amfani da sanda. Idan aka ga na kara girma, sai a canza min sandar kwatankwacin tsawona. Daga baya ma sai na koyi yadda ake yin sandar, yanzu haka a duk lokacin da nake bukatar canja sanda da kaina nake yin abata.” Inji shi.
Kabiru ya shaida wa Aminiya cewa bai sami damar ci gaba da karatunsa ba saboda yanayin rayuwa, don haka sai ya zabi sana’ar walda inda ya rika zuwa wurin wani mutum mai suna Yakubu mai walda a unguwar Ja’oji yana koyo. “Ga shi yanzu ina yin walda na zama maigidan kaina. Alhamdulillahi, a yanzu haka ma ana dauka ta aiki zuwa gari-gari in je in gudanar da aikin walda. Kin ga rashin kafa bai hana ni neman na kaina ba.” Inji shi.
Baya ga aikin walda da suke gudanarwa a gareji inda ake kawo musu aiki, inji Kabiru Sabo, sukan je gidaje ko ofis-ofis su gudanar da aikinsu na walda.
Ya ce, “Baya ga ire-iren ayyukan da mutane ke kawo mana a gareji inda muke yi musu aiki, wannan ya hada da aiki mai yawa da kuma wanda ake ba mu kwangilar yin su, akan nemi mu gudanar da aiki a gida. Sai dai cajin kudin da muke karba a kan ayyukan da ake daukar mu a gida ya fi na wanda ake kawo mana gareji, saboda a wannan aiki za mu caji mutum kudin mota ga kuma janareta da za mu dauka mu tafi da shi don yin aikin”.
Malam Kabiru ya bayyana cewa sana’ar walda sana’a ce mai riba sosai, domin da ita ya yi aure har ya mallaki gidan kansa. Ya shekara 16 yana gudanar da sana’ar, wadda ya ce ya samu ci gaba mai yawan gaske, musamman da yake yana taimaka wa iyayensa da ’yan uwansa daga abin da yake samu yau da gobe. Kuma mutane da dama sun koyi sana’ar a wurinsa.
Dangane da kalubalen da ke damfare da sana’ar, Malam Kabiru ya koka ne kan rashin wutar lantarki, wanda babban lamari ne, wanda ya ce, “A duk lokacin da muka tashi babu wuta, to fa ba aiki, kodayake yanzu mun samu wata ’yar mafita ta janareta wajen gudanarwa, domin idan mutum ya tsaya jiran wutar lantarki, sai sana’ar ta mutu murus. Amma idan da aiki a kasa ga kuma wuta, to fa ba mu ganin wahalar aikin ko kadan”.
A karshe Malam Kabiru ya yi kira ga nakasassu ’yan uwansa, musamman wadanda suke amfani da nakasarsu wajen yin bara, su fahimci kasancewar mutum yana da nakasa ba shi ke nufin sai ya yi bara zai ci abinci ba. “Idan Allah Ya tauye mutum a wani bangare na jikinsa, Yana ba shi wata basira ta daban, wacce idan ya yi amfani da ita, zai mori kansa. Saboda haka nakasassu ya kamata su nemi sana’ar yi, domin ga sana’o’i nan birjik, ba lallai sai wacce za a yi amfani da karfi ba. Akwai sana’ar da kana zaune za ka ci abinci daga gare ta. Addinin Musulunci ma bai yarda da bara haka kawai ba. Sai dai kuma gwamnati ya kamata ta rika taimaka wa nakasassu wajen samar musu da aikin yi ko kuma ta ba su jarin da za su rika jalaftawa suna neman na kansu”. Inji shi.