✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da na so zan nemi wa’adi na uku —Obasanjo

Na san duk wata hanya ta neman wa'adi na uku amma ban nema ba.

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya ce da ya so da ba abinda zai hana shi neman wa’adi na uku bayan kammala mulkinsa a shekarar 2007.

Obasanjo ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, a wani taro na yanar gizo da wata kungiya mai rajin tabbatar da jagoranci na gari a Afirka.

Obasanjo ya yi ikirarin cewa yana da cikakkiyar damar iya ci gaba da mulki a wa’adi na 3 amma sam ba shi da sha’awar tsawaita mulkinsa dalilin kenan da ya sanya shi sauka a wancan lokaci.

Tsohon shugaban na Najeriya ya musanta jita-jitar da ta karade kasar a wancan lokaci na cewa ya so ya ci gaba da mulki a wa’adi na 3, yana mai cewa ko shakka babu idan har da ya so hakan to da wani zance ake yi ba wannan ba.

“Ban taba neman Shugaban Kasa bayan kammala zango na biyu na mulkina ba.

“Da ina so, ina da ikon sanin hanyoyin da zan yi hakan”, in ji shi.

Obasanjo wanda a baya-bayan nan ya fito fili ya goyi bayan dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar LP wato Peter Obi, ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen gamsar da ‘yan Najeriya don ganin sun juya wa jam’iyyun PDP da APC baya a zaben da ke tunkarowa cikin watan gobe.c

Sai dai ya ce ba shi da aniyar shiga sahun masu yakin nema zabensa, kasancewar ba ya cikin kowacce jami’iyya a yanzu.

Haka zalika, kan batun Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kuwa, Obasanjo ya ce yana matukar bukatar gyara, domin akwai ’yan kurakuran da ba a rasa ba a cikinsa.

“Wasu mutanen koda yaushe sai su dora laifin komai da ya faru a kasar nan kan Kundin Tsarin Mulki.

“Na yarda Kundin na da guraben cikewa, amma na wace kasa ce ya ke daidai dari bisa dari? Don haka akwai bukatar gyara wasu sassansa,” in ji shi.

Obasanjo ya kuma ce bangaren da ya fi ko’ina bukatar kwaskwarima shi ne na batun mulkin kasar daga hannun shugabanninta.