✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da ladan Sule da Sisi na fara aikin jarida – Kabiru Fagge

Alhaji Kabiru Fagge, tsohon ma’aikacin gidan Rediyon Muryar Amurka da ya yi aiki a gidajen jaridu da rediyo da talabijin. Kuma ya taba koyarwa da…

Alhaji Kabiru Fagge, tsohon ma’aikacin gidan Rediyon Muryar Amurka da ya yi aiki a gidajen jaridu da rediyo da talabijin. Kuma ya taba koyarwa da wallafe-wallafen littattafai. A hirarsa da Aminiya a Unguwar Fagge da ke cikin birnin Kano, ya bayyana yadda ya fara aikin jarida a kan albashin sulai da sisi, kuma ya tabo wasu al’amuran da suka shafi rayuwarsa:

Mene ne takaitaccen tarihinka?
Kabiru Fagge: Sunana Muhammad Kabiru Fagge, an haife ne ranar 12 ga Satumba, 1946. Kamar yadda aka saba a rayuwar Bahaushe na shiga makarantar allo inda na shafe shekara bakwai ina karatu, kuma Alhmadulillahi na sauka, bayan na sauka na zo da hadda har aka samu izu uku a haddar. Bayan nan sai aka sanya ni makarantar firamare ta Baptist da ke Sabon Gari, a lokacin ana kiranta makarantar Yarbawa zalla, saboda, akwai kuma Holy Trinity, wadda ake kiranta makarantar Ibo zalla. Sai ka fara zuwa Holy Trinity sannan za ka je Baptist. Duka-duka dai, sai babana ya ce, abin da za a yi kawai in koma Fagge. Sai na dawo makarantar firamare ta Fagge. Daga makarantar firamare ta Fagge bayan na kammala aji hudu zuwa biyar, sai na dauki jarrabawar zuwa makarantar midil, na ci, sai na tafi wannan makaranta da ke Yakasai. Ana haka maimakon na tafi midil din, sai aka raba midil; wasu suka tafi Gwale, wasu suka tafi Kuka. Sauran sai aka bar su a can middil din, ni kuma sai na ta fi Kuka. A Kuka ne na sake daukar jarrabawa, duk da cewa shekaruna sun dan zarta, maimakon in tafi Kwalejin Gwamnati a Zariya ko Kano, sai aka ce in tafi Kwalejin Horon Malamai (GTC); da ke Wudil, sa aka ce ga wata sabuwa an bude a Bichi, mu je mu fara da ita. Nan na samu shekara biyu, na dauki jarrabawa na ci. A kwalejin Horon Malamai ta Bichi (Bichi Teachers College) sai da muka shekara biyar muna yi, har da koyarwar gwaji muka gama, muka dauki jarrabawar malami mai daraja ta biyu (Grade II). A wancan lokacin kowa zai gaya maka cewa jarrabawar Grade II tana da dan wahala. Bayan ka gama jarrabawa, sai ka fito ka fara koyarwa, ka jira sakamako. Muka fito, aka warwatsa mu a makarantun firamare, inda aka kai ni makarantar firamare ta Tudun Wada da ke hanyar Bompai. Bayan wata shida aka ba ni Hedimasta. Sai na koma makarantar ATC/ABU, don neman NCE, lokacin nan Jami’ar Ohio, sun fara zuwa suna yin aikin taimakon al’umma, a karkashin kungiyarsu ta “Peace corp” suka zo daga Amurka suka rika koya mana. Sai na yi sha’awar Peace corp, don haka na shiga cikinsu. Domin sun zo da isassun kayan aiki, na ban mamaki, ta haka muka fahimci yadda ake koyarwa. Wadanda suka shiga za su tafi Amurka su yi karatu, sai na kasance daya daga cikin wadanda aka zaba a 1958.
Bayan mun fito daga Babbar Kwalejin Horon Malamai ta ATC/ABU, sai aka ce ai ba malamai, mu fito kawai mu zo mu fara koyarwa, don haka na koma Kwalejin Horon Malamai ta Bichi. Da na ga abin ana ta kai da komowa, inda aka sake mayar da ni makarantar firamare ta Tudun Wada, ana ma shirin a mayar da ni can karamar Hukumar Tudun Wada, mai iyaka da Filato. Sai na yi wuf, na je na dauki jarrabawar share fagen shiga jami’a (Pre-lume). Bayan shekara uku muna wannan karatu na Pre-lume, na kasance daya daga cikin wadanda suka samu nasara. Sai na ce ni ina son karanta darussan addinin Musulunci, duk da cewa matasa ba sa son karanta wannan fanni. Sai aka yi dabara, aka rika koyarwa da Turanci, amma karatun Alkur’ani da tafsiri duk da Larabaci aka rika koyar da su. Tarihini Musulunci da tarbiyya a Turanci. Ina cikin karatun digirina, sai karamar hukuma ta ce ba ta yarda ba, ni ma’aikacinta ne. Da digirina na farko aka sake mayar da ni firamare na ci gaba da koyarwa.
Aminiya: Alhaji da yake aikin jarida ne ya sanya ka yi fice, shin ta yaya aka fara?
Kabiru Fagge: Tun daga makarantar firamare na fara sha’awar aikin jarida. Don haka na fara da Daily Comet. Malam Tanko Yakasai shi ya zo makarantarmu, wato babbar firamare ta Kuka inda nake koyarwa, ya nemi masu sha’awar rubutun Hausa a Daily Comet. Da ma Daily Comet din gaba dayanta shafi hudu ce, tsakiya ne shafin Hausa, kuma Tanko Yakasai ne Editanta. Kuma tsallakowa za ka yi daga hedkwatar NEPU sai Kuka; da ya tsallako, sai ya ce su wane ne masu sha’awar aikin? Sai na ce ga ni, muka shiga. A lokacin ana ta la’antar aikin jarida, cewa akwai karya da wace tsiya. Muka shiga, ya ce da mu ga shafin nan, shafin Hausa ku rika taimakawa. Duk shafi in labarinka ya fito Sule da Sisi. Sai na rika rubuta labarai kamar yadda kake yi din nan. Duk mako sai na zabi wata makala kan wani darasi in yi rubutu a kai. Ka ji ta yadda aka fara.
Aminiya: Daga wannan aiki na jaridar Daily Comet, ka ci gaba da yi wa wasu jaridu na cikin gida, ko kuwa sai kasar Amurka?
Kabiru Fagge: Daga Daily Comet sai Northern Star (Jaridar Jam’iyyar AG). Ita kuwa Daily Comet ta NEPU ce. Kuma ’yan Fagge a lokacin, kusan in ce duk ’yan NEPU ne. Har iyayenmu NEPU suka yi. Saboda haka dai muka yi can. Dauda dangalan suka tura mu. Don su ne yayyenmu da su Mudi Spikin. Kuma su suka matsa kan lallai sai iyayenmu sun tura mu makaranta.
Aminiya: Yaya aka yi ka kama aiki da gidan Rediyon Amurka?
Kabiru Fage: Daga Daily Comet har zuwa Gaskiya Ta Fi Kwabo, akwai rubuce-rubucen da muka yi. A lokacin duk mako in Gaskiya Ta Fi Kwabo za ta fito sai ka ga labarina. Lokacin Usman Mairiga shi ne Editanta, ina da shafi a jaridar har zuwa cikin shekarun 1980. Shi wannan Edita namu, ya zo ya dauke ni, na tafi Kaduna, da na tafi Kaduna, na ga akwai matsala a dattawanmu, wadanda Hausa ce suka iya tsagwaronta. Don haka da muka zo da digiri a Hausa, sai muka fahimci cin gyara na hada mu rigima da tsofaffi da suke ganinmu yara, har ma sukan ce wannan yaro wane irin ne wannan da zai gwada mana Hausa? Da na ga irin wannan abu ba zai yiwu ba, tunda yake ci gaba ake nema, sai na bar Kamfanin New Nigerian, wato mai buga jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, a lokacin nan an bude gidan talabijin. Audu Bako ya bude NTb, sai ya je Kaduna ya ce duk wani mutumin Kano (da ke aiki a wata kafar watsa labarai) ya dawo. Sai ya kwaso mu ya kawo mu NTb, inda muka fara aiki da NTb. Mun yi aiki da NTb na shekara biyu.
Aminiya: To yaya aka yi ka kama aiki da gidan Rediyon Muryar Amurka?
Kabiru Fagge: Yadda na shiga Rediyon Muryar Amurka, shi ne na rika aika musu da rahoto. Kuma tun ina makaranta na taba nuna musu sha’awata game da aikinsu. Sai ya kasance akwai USIS a nan, kuma duk Arewa nan kadai suke da ofis. Da na fara zuwa nan, sai na mika takardun neman aiki. Daga nan na fara samun horo da gwaji da keken rubutu. Sai muka dauki jarrabawa, muka ci. Zan tafi sai karamar Hukuma ta ce ba ta yarda ba, ni ma’aikacinta ne. Bayan shekara biyu sai na dauki wata jarrabawar kai-tsaye zuwa Amurka, na yi sa’a kuma na ci. Domin a wancan lokacin duk shekara ne sai sun turo a yi jarrabawar daukar ma’aikata. Za ka ji wani ana ce da shi Barry Barges. Duk yana zagayawa yana neman wadanda za su yi aiki da Muryar Amurka. Sai na ce ina so, bari in dauki jarrabawar ka ji yadda aka yi ke nan.
Aminiya: Alhaji da yake ka shafe shekaru a wannan kafar labarai, yaya za ka kwatanta aikin jarida a Najeriya da kasar Amurka?
Kabiru Fagge: Aikin jarida a Najeriya da a kasar Amurka, zan iya kwatanta shi da cewa, yanzu kam Najeriya tana tasowa, amma sam-sam ba za a iya kwatantawa ba, wajen maganar ’yanci da walwala. Sai dai duk da haka, ’yanci da walwalar bai hana in ka rubuta labari na batanci nan take su kama ka. Kuma shi wanda ka bata wa suna nan take ya kai ka kotu. Gaskiya dai ’yanci da walwala a aikin jarida sai Amurka.
Aminiya: Alhaji wasu littatafai da ka taba wallafawa, wato jagoran Malamin Firamare da wakokin Alhaji Mamman Shata, za mu so jin ko me suka kunsa a takaice?
Kabiru Fagge: Jagoran Malamin Makarantar Firamare dai ya faru saboda kwadayi da nake da shi a kan koyarwa. Na jawo hankalin ’yan uwana malaman makaranta su dukufa ka’in da na’in kada kwadayin Turanci ya ja su, su watsar da harshenmu na Hausa. Idan kuma za su koyi Turancin, to su bi ta yadda muka koya, wato daga Hausa zuwa Turanci (Hausa–English). Don ta nan ne muka ga shehunan malamanmu irin su Shehu Minjibir suka koyar da mu.
Shi kuma Alhaji Mamman Shata tarihi ne, domin lokacin Jibo dan Maimota, Allah Ya jikansa, makwabcinmu ne, ga gidansu, ga gidanmu, idan Shata ya zo Kano, to a gidan Jibo yake sauka. Duk sa’adda zai yi wasa, sai in fito daga gidanmu in zauna, ana dan jefo min kwabo wai ni ne yaron Shata, ni dai kawai kwabon nake so. Idan na dan tattara sai in gudu. To tun daga lokacin nan nake da sha’awar Shata. Wannan shi ne dalilin da ya sanya na rubuta tarihin Shata. Kuma wannan bayani da na yi maka ya auku ne a 1953. Sannan a lokacin Shata ya taba cewa ni dansa ne. Muddin Shatan yana nan ni ne dan aike. A lokacin ya fi cin tsire, shi ne abincinsa. Ni ke zuwa ina sawo masa tsire da garin kwaki.
Aminiya: Wacce shawara za ka bai wa ’yan jarida ko masu son koyon aikin?
Kabiru Fagge: Shawarar da zan bayar ita ce hakuri da kuma juriya. Bayan an hakura kuma a rika bin sawun labari, don tantance gaskiya, kafin a tabbatar da shi. Ba wai daga ganin labari ka yi sauri ka bayar ba, a’a, sai ka samu hakikanin gaskiyarsa. Kiyaye duk wata ka’ida da ke tabbatar da labari kan sanya a samu cikakken rahoto, wanda za a iya kira da sunan labari kuma mai kima.