✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kaina na ajiye shugabancin Gidan Rediyon Albarka – Musa Waziri Hardawa

Tsohon Janar Manajan Gidan Rediyon Albarka Rediyo mai zaman kansa na FM, da ke Bauchi Alhaji Musa Waziri Hardawa ya ce labarin da ake yadawa…

Tsohon Janar Manajan Gidan Rediyon Albarka Rediyo mai zaman kansa na FM, da ke Bauchi Alhaji Musa Waziri Hardawa ya ce labarin da ake yadawa cewa an kore shi daga aiki saboda rahoton da aka yi kan bada kwangilar Naira biliyan 3.6  da ake zargin Gwamnan Jihar Bauchi da ba wa kamfanin da yake rike da darakta ba haka ba ne.

“Ni ma na ga wannan labari, amma akwai kura-kurai da yawa a ciki. Gaskiya na bar wajen, amma ba don saboda wannan rahoto da gidan rediyon ya dauka kan wannan kwangila ba ne. Kawai dai na gaji ne, kuma shi Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Dokta Ladan Salihu, wanda wajensa ne in zan bari ya kamata ya sani, shi ne muka daidaita da shi cewa zan bar wajen,” inji shi.

Ya ce “Wanda aka ba Janar Manajan ma yanzu shi ne ya yi labarin, ka ga inda don haka ne da an kore shi. Kuma ni ban ma san labarin ba, daga baya nake ji, kuma shirin ma ba wai yana sukan gwamnati ba ne, abin da shirin yake cewa ya bi diddigin yadda labarin ya fito ne, inda ya ce, “In har bada wannan aikin kwangila da gaske ne mene ne kuskuren gwamnati a ciki?”

Jarida Intanet ta Premium Times ce ta yi rahoton, zargin Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir da bada kwangilar sayen motocin alfarma 105 kan Naira biliyan 3.6  ga kamfanin da yake jari a ciki kuma yake darakta,  inda ta ce yin hakan ya saba wa ka’idoji da dokokin bayar da kwangila. Tuni gwamnatin jihar ta karyata zargin inda ta ce ta bi dukkan ka’idoji wajen bayar da kwangilar kuma Gwamnan bai da jari a kamfanin..

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Dokta Ladan Salihu mamallakin Gidan Rediyon Albarka kan lamarin amma ba ta samu nasara ba.