✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?5

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya…

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan a ce kai ne Al-mustapha, ko za ka iya yafe wa wadanda suka yi sanadiyyar jefa ka cikin wannan ukuba? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka bayyana dangane da haka:

Zan iya yafewa – Musa Yusuf
Malam Musa Yusuf: “A ganina, in da ni ne Manjo Janar Hamza Al-mustapha, ko shakka babu zan yafe wannan cin zali da aka yi mini; kasancewar Allah (SWT) Ya kaddara hakan sai ta same ni. Don in ba don kaddarar da ta fada ba, da babu yadda za a yi in shiga wannan hali na kuntatawa tamkar ina bauta, alhali ina mutum mai cikakken ’yanci kamar kowane dan kasa.
“Don haka, in har da ni din ne, ni ma yafewa zan yi kamar yadda shi ya ce ya yafe; don fadar Allah (SWT) cewar, in an yi maka abu ka rama kwatankwacinsa amma da za ka yafe shi ya fi. A karshe Allah (SWT) ya ce lallai yana tare da masu hakuri.”