✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?2

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya…

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan a ce kai ne Al-mustapha, ko za ka iya yafe wa wadanda suka yi sanadiyyar jefa ka cikin wannan ukuba? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka bayyana dangane da haka:

Ba zan yafe musu ba – Ila Mai Shayi
Ila Mai shayi (Gbazabgo): “A gaskiya da ni ne Al-mustapha, ba zan yafe wa wadanda suka yi mani wannan makarkashiya ba; domin kuwa sun cutar da ni matuka. daya daga cikin cutar da aka yi masa ita ce, an tsare shi ba da hakkinsa ba, har mahaifiyarsa ta mutu bai gana da ita ba. Haka kuma an sanya iyalansa cikin kunci na tsawon lokaci. Ga shi kuma an takura wa rayuwarsa, ta yadda aikinsa da al’amuransa na rayuwa suka dagule. Babu shakka an cutar da shi bisa zalunci kuma da gangan. Wannan dalili ne ya sanya na ce da ni ne shi, ba zan yafe wa duk mai hannu ga kuntata mani ba. Amma Al-mustapha ya yi jimiri, ya cika mai hakuri da har ya ce ya yafe masu.”