✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?1

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya…

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan a ce kai ne Al-mustapha, ko za ka iya yafe wa wadanda suka yi sanadiyyar jefa ka cikin wannan ukuba? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka bayyana dangane da haka:

Zan iya yafe musu – Umar Muhammad
Umar Muhammad: “Da ni ne Al-mustapha, babu shakka zan iya yafe wa mutanen da suka yi mani sanadiyyar shiga kurkuku, domin kuwa komai mukaddari ne daga Allah. Kuma ita rayuwa ai jarabawa ce. Duk abin da Allah Ya kaddara, babu mai iya canja shi. Ganin yadda shi kansa Al-mustapha ya ce ya yafe masu, to lallai ya burge ni sosai kuma hakan ya nuna cewa shi ya cika mutum mai kirki da sanin ya kamata.”