✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da kai ne Al-mustapha, za ka yafe wa wadan su ka zalunceka?

A makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya…

Alhaji Abdu Tudun WadaA makon jiya ne kotu a Legas ta wanke Manjo Al-mustapha daga zargin da ake masa na kashe Kudirat Abiola kuma ta sallame shi ya koma gida, bayan daurin da aka yi masa na tsawon shekara kusan 15. Ana zargin wasu ne suka yi masa makarkashiya da kazafi. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan a ce kai ne Al-mustapha, ko za ka iya yafe wa wadanda suka yi sanadiyyar jefa ka cikin wannan ukuba? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka bayyana dangane da haka:

Ba zan taba yafewa ba
– Alhaji Abdu
Alhaji Abdu Tudun Wada: “A gaskiya in har da ni ne Manjo Janar Hamza Al-mustapha, ba zan taba yafe wa duk wadda ke da hannu wajen ci mini irin wannan zarafi ba haka siddan, ba a kan hakkina ba. Don ganin cewar babu hakkina a kan wannan irin tataburza a dukkan kotunan da aka zaga na tsawon shekaru 15, wadda a karshe kotu ta ce ta yi sallama tun da ba ta samu wani takamammen laifi ba; dama kuma duk duniya ta san an yi irin wannan cin mutunci ne bisa wata manufa. Saboda haka a gare ni, tabbas in da ni ne Al-mustapha babu batun yafiya a kan irin wannan halayya ta nuna rashin tausayi, wadda a tarihin kasar nan ba a taba samun mutumin da aka ci masa zarafi ba da danne masa hakki haka kurum kamar wannan bawan Allah ba. Don haka duk wanda ya ce zan yafe wa, watakila mafarki mai shi yake yi.”