✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da goyon bayan al’umma ta’addanci ke yaduwa- Kwamandan Soja

Kwamandan Makarantar Kimiyyar Makamai na Sojojin Ruwa ta Najeriya da ke garin Kachia a jihar Kaduna (NNSAT) Real Admiral Tanko Yakubu Pani, ya bayyana saken…

Kwamandan Makarantar Kimiyyar Makamai na Sojojin Ruwa ta Najeriya da ke garin Kachia a jihar Kaduna (NNSAT) Real Admiral Tanko Yakubu Pani, ya bayyana saken da jama’a ke yi da nuna halin ko in kula a matsayin dalilin kutsowa da kuma yaduwar ta’addanci a cikin al’umma.

Kwamandan, ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake karbar lambar yabo daga jama’ar yankin masu kishin garin Kachia da su ka kai masa ziyara a barikin, saboda kokarinsa wajen dakile ayyukan batagari a yankin Kudancin Kaduna.

Lokacin ake mikawa Kwamandan lambar yabo

Ya bayyana ayyukan batagari a matsayin babban barazana ga zaman lafiya, inda ya ce mafi akasarin batagarin na zaune ne a cikin al’umma kuma ana rayuwa tare da su a matsayin ‘yan uwa da dangi ko kuma baki, inda ya yi kira ga al’umma da su tashi tsaye tare da baiwa dukkanin jami’an tsaro hadin kai da goyon baya ta hanyar sanar da su dukkanin labarin da ka iya taimaka musu wajen tsamo baragurni daga mafakarsu.

A karshe ya nuna godiyarsa ga jama’ar da su ka karrama shi tare da shan alwashin kara zage damtse wajen maida garin na Kachia a matsayin wacce za ta kubuta daga ayyukan batagari.