✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sunday Igboho na da alaka da Boko Haram —Malami

An gano alakarsa da wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai dai rai kan ta'addanci.

Gwamnatin Tarayya ta bankado asusun ajiya 43 da Sunday Igboho yake amfani da su a wasu bankuna tara wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce Sunday Igbho yana amfani da asusun bankunan ne wajen tara kudaden daukar nauyin ayyukansa na neman ballewa daga Najeriya daga hannun iyayen gidansa, cikinsu har da wani dan Majalisar Dokoki ta Kasa a halin yanzu.

Wata sanarwa da ministan ya fitar ta ce Sunday Igboho, wanda sunansa na asali Sunday Adeyemo, ya kashe sama da Naira miliyan 200 daga 2013 zuwa 2021 da sunan kamfaninsa, Adesun International Concept.

“Gwamnatin Tarayya ta samu rahoton hadahadar kudaden Adeniyi Sunday Adeyemo, wato Sunday Igboho, wanda aka gano cewa darakta ne kuma mai sanya hannu a ciri kudade a kamfanin Adesun International Concept Limited, wanda aka yi wa rajisata ranar 23 ga watan Afrilu, 2010.

“Sauran daraktocin kamfanin su ne Oladele Oyetunji da Aderopo Adeyemo. Sunday Igboho na da akala da asusun ajiya 43 a bankuna tara,” inji Malami.

“Igboho ya karbi jumullar kudi Naira miliyan 127 da dubu 145 a tsakanin ranar 22 ga Okotoba, 2013 zuwa 28 ga watan Satumba, 2020 ta asusun ajiyar kamfanin.

“Ya kuma fitar da Naira miliyan 273 da dudu 198 da 200 daga asusu bankin nasa a tsakanin ranar 15 ga watan Maris, 2013 zuwa ranar 11 ga watan Maris, 2021.

“Binciken ya kuma gano cewa kamfanin Adesun International Concept Ltd (mallakin Igboho) ya tura Naira N12, 750,000 wa kamfanin Abbal Bako & Sons.

“Kamfanin Abbal Bako & Sons da mai shi, Abdullahi Umar Usman na daga cikin mutanen da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda da kudade.

“Abdullahi Umar Usman na da alaka ta kudi da Surajo Abubakar Muhammad wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) bayan samun shi da laifin taimaka wa ’yan ta’adda (Boko Haram) da kudade.

“Wannan rahoton ke nuna irin alakar da ke tsakanin karajin nema ballewar Igboho daga Najeriya da ta’addanci da kuma neman tayar da zaune tsaye a Najeriya.

“Rahoton ya kuma gano alakar cinikayya tsakannin kamfanin Adesun International Concept Ltd (na Igboho) da wasu kamfanonin gine-gine da sauransu.

“Duk da samun wannan rahoton, Gwamnatin Tarayya a tsaye take, kai da fata wajen tabbatar da aminci a Najeriya.

“Za kuma ta yi duk abin da ya kamata a bisa doka, wajen ba wa wannan al’amari muhimmancin da ya dace, tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi,” inji sanarawar.

%d bloggers like this: