Matar Gwamnan Jihar Kaduna, Asia El-Rufai, ta ce babu kudin fansar da za a biya idan ’yan bindiga suka yi garkuwa da ita.
Asia El-Rufai ta shaida wa wani taron horarwa kan tsaro da zaman lafiya da wata kungiya ta shirya a Kaduna, cewa lallai ne ’yan Najeriya su sadaukar da kansu domin kawo karshen garkuwa da mutane.
- Malaman kwalejin kimiyya da fasaha sun janye yajin aiki
- Buhari ya amshi wayar hannu ta farko da aka kera a Najeriya
“A shirye nake in mutu a hannun masu garkuwa da idan har hakan zai kawo zaman lafiya a kasar nan.
“Idan har muka ci gaba da biyan kudin fansa, tamkar kana zuba wa wuta makamashi ne, kana bai wa ’yan bindiga da masu garkuwa kudi domin su sayo makaman da za su ci gaba da farautar ka.
“Bai dace ba mu ci gaba da biyan kudin fansa ba sam; Wannan ra’ayina ne,” inji Asia El-Rufai wadda malama ce a Jami’ar Baze da ke Abuja.
Ta ci gaba da cewa, “Na fada a baya kuma zan kara nanatawa, idan an yi garkuwa da ni, to kada wanda ya biya kudin fansa; Maimakon haka ku yi mini addu’a, in mutuwata ce ta zo to Allah Ya sa in cika da imani, in kuma zan fito to kada a ci zalina.
“Idan muka ci gaba da ba su kudi suna zaluntar mutane, tabbas ba za su daina ba,” inji ta.
Matar gwamnan wadda ita ce Babbar Bakuwa a wajen taron ta ce dole ne ’yan Najeriya su koma rayuwa cikin zaman lafiya kamar yadda suke a da kuma mata na da muhimmiyar rawar da za su taka domin cimma hakan.