Wata cuta da take kone ganyen Dankalin Turawa tare da rubar da ’ya’yan da ya yi a kasa da ake kira cutar Zanzanar Dankalin Turawa, ta jawo wa manoman dankali asara a bana, musamman a Jihar Filato da ta yi fice wajen noman dankalin a kasar nan.
Har ila yau wata babbar matsalar da manoman dankalin suka fuskata a bana, ita ce ta tsadar irin dankalin.
- Ta yi wa kanta allurar jinin saurayinta mai kanjamau don nuna masa soyayya
- Kafofin watsa labarai 52 da NBC ta soke lasisinsu
Wasu manoman Dankalin Turawa da Aminiya ta tattauna da su, sun bayyana cewa a farkon watan Afrilu da Mayun bana da suka fara dashen irin dankalin, sun sayi buhun irin a kan Naira 20,000 zuwa 22,000 maimakon Naira 15,000 da suka saya a bara.
Manoman sun ce, idan aka yi la’akari da wadannan matsaloli da suka fuskanta a daminar bana, zai yi matukar wahala su mayar da kudaden da suka kashe, balle su kai ga cin riba.
Wata mai noman Dankalin Turawa, mai suna Misis Atong James da ke da gona a Lamingo, a Karamar Hukumar Jos ta Arewa, ta ce, a farkon daminar bana ta dasa irin Dankalin Turawa buhu biyu da rabi a gonarta, amma zai yi wuya ta samu buhun dankali daya a gonar.
Ta ce, a baya idan ta dasa irin Dankalin Turawa buhu biyu zuwa buhu uku tana samun buhu 12 zuwa buhu 15.
Ta kara da cewa, ta dakatar da hakar dankalin saboda duk wanda ta hako, sai ta ga ya rube.
Don haka ta mayar da hankali ga noman albasa da masara da barkono da rogo da kuma kabeji da take yi.
Ta yi gargadin cewa, bisa ga dukkan alamu, idan har gwamnati ba ta dauki wani mataki ba a kan wannan lamari, irin dankalin da za a dasa a noman rani mai zuwa zai yi matukar tsada.
Shi ma a zantawarsa da Aminiya, wani manomin dankalin mai suna Bitrus Mador, ya ce, mafiya yawan manoman da annobar ta rutsa da gonakinsu, sun dasa dankalin ne daga watan Mayu zuwa watan Yunin da ya gabata.
Amma manoman da suka dasa dankalinsu a watan Afrilu, annobar ba ta shafi gonakinsu ba. Ya ce, sun gano ruwan sama mai yawa ne yake yada wannan annoba.
Don haka, manoman da suka dasa dankalinsu daga watan Mayu zuwa watan Yuni ne suka fi fuskantar annobar, saboda a lokacin an fara ruwan sama mai yawa.
Ya kara da cewa, manoman Dankalin Turawa da dama sun yanke shawarar cewa, a damina mai zuwa ba za su yi noman Dankalin Turawa ba, saboda asarar da suka yi a bana.
Don haka sai an dauki matakan magance annobar a damina mai zuwa.
Da yake tabbatar da barkewar annobar, Shugaban Kungiyar Manoma ta Gangare a garin Jos, Dayyib Zachariah, ya bayyana cewa, manoman Dankalin Turawa da dama sun fuskanci wannan annoba a Jihar Filato.
“Babu shakka mamakon ruwan da aka rika yi ne ya taimaka wajen yada wannan annoba.
“Don haka, muna shawartar manoma a duk lokacin da suka ga irin wadannan matsaloli sun taso a gonakinsu, su fito su yi magana don a ba su shawarwarin da za su magance su,” inji shi.