Akalla mutum miliyan 13 na fuskantar barazanar kamuwa da cutar tamowa a kasashen Somaliya da Habasha da kuma Kenya a cikin ’yan watanni masu zuwa.
Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce barazanar ta karu ne a sakamakon kimanin shekara 1o da aka kwashe ana fama da tsananin fari a Gashin Afirka.
“Amfanin gona da dabbobi suna mutuwa, yunwa sai karuwa take yi saboda karancin ruwan sama a Gabashin Afirka,” inji sanarwar da jami’in hukumar na yankin, Michael Dunford, ya fitar.
Shekara uku ke nan a jere da ake fama da karancin ruwan sama a kasashen uku, kuma rabon da a samu karancin ruwan sama haka tun shekarar 1981.
Karancin ruwan sama ya yi sanadiyar mutuwar amfanin gona da dabbobi fiye da kima, wanda ya da sa yawancin al’ummomin makiyaya da manoma yin kaura daga yankunan, saboda rashin wurin yin noma ko kiwo.
Uwa uba an yi hasashen cewa za a kara samun karancin ruwan sama a bana a yankin Gabashin Afirka, kamar yadda Dunford ya bayyana.
Ya ce, “Yanayin na bukatar a gaggauta daukar matakai domin ceto rayuwar al’umma,” domin kauce wa maimaituwar ibtila’in da ya farua a Somaliya a 2011 inda mutum 250,ooo suka rasu a sakamakon matsananciyar yunwa da fari ya haifar.”
A halin yanzu dai ana rabon kayan abinci a wasu yankunan kasashen Kenya, Habasha da Somaliya inda mutum miliyan 13 ke fama da cutar tamowa.
Akwai hasashen cewa matsananciyar yunwa za ta addabi yankin a cikin wata ukun farkon shekara da muke ciki ta 2022.
Mutum miliyan 5.7 ne dai ke bukatar agajin abinci a yankunan Kudanci da kuma Kudu maso Gabashin kasar Habasha, inda ke da kananan yara da matsa 500,000 masu fama da cutar tamowa.
A Somaliya kuma, ana hasashen yawan mutanen da ke fama da tsanananin yunwa za su karu daga miliyan 3.5 zuwa miliyan 4.6 daga yanzu zuwa watan Mayu, muddin ba a dauki kwararan matakai cikin gaggawa ba.
A yankin Arewaci da kuma Kudu maso Arewacin Kenya, mutun miliyan miliyan 2.8 na bukatar agaji, tun bayan da aka ayyana dokar ta-baci saboda farin da aka samu daga watan Satumban 2021.
Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar Dala miliyan 327 domin daukar matakan gaggawa na tsawon wata shida masu zuwa domin taimaka wa al’ummomin manoma da makiyaya ta yadda za su iya jure wa matsalolin da suka gandanci sauyin yanayi.