✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar pneumonia ta kashe yaran Najeriya dubu 162 a 2018 – UNICEF

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce a tsakanin kasashen duniya, Najeriya ce ta fi yawan yaran da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar pneumonia. Hukumar…

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce a tsakanin kasashen duniya, Najeriya ce ta fi yawan yaran da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar pneumonia.

Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar, UNICEF, ta wallafa, cewa a shekarar 2018 an kiyasta yaran Najeriya dubu 162 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar (wato yara 443 a kullum, ko kuma yara 18 a duk sa’a guda).

Baya ga Najeriya da aka kiyasta mutum 162,000 da suka mutu, kasashen da ke kan gaba wajen mutuwar yara sakamkon cutar sun hada da Indiya 127,000 da Pakistan 58,000 da Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo 40,000 da kuma Habasha 32,000.

Sauran kasashen su ne: Indonesiya 19,000, China 18,000, Cadi 18,000, Angola 16,000, Tanzaniya 15,000, Somaliya 15,000, Nijar 13,000, Mali 13,000, Bangladesh 12,000, Sudan 11,000.  Jimilla a duniya 802,000. Kamar yadda Hukumar UNICEF ta bayyana jerin kasashen da cutar pneumonia ta fi kisan yara ‘yan kasa da shekara biyar a 2018.