✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Lassa tana kara yaduwa a Najeriya

Bullar cutar Lassa da aka ruwaito daga shekaranjita zuwa jiya na kara yaduwa a fadin Najeriya. A farko, an samu bullar cutar ce a Jihar…

Bullar cutar Lassa da aka ruwaito daga shekaranjita zuwa jiya na kara yaduwa a fadin Najeriya.

A farko, an samu bullar cutar ce a Jihar Kano da Ondo, inda aka ruwaito cewa mutum 16 sun mutu a Ondo, 3 suka mutu a Kano.

Yanzu kuma an samu bullar cutar a Enugu da Delta da Bauchi da Edo da sauransu.

A yanzu dai an tabbatar da rahotannin mutum 121, 89 a Ondo, 18 a Edo, 5 a Ebonyi, 5 a Taraba, 2 a Filato, Bauchi da Ogun guda daya-daya, sai Kano da mutum 3 suka mutu.

A bara ma an samu bullar cutar, inda ta kashe mutum 10, amma ya zuwa yanzu kadai, akalla mutum 21 ne suka mutu.