✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar kyandar Birrai ta barke a jihohi shida

Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta ce an samu rahoton bullar kwayar cutar da ake zaton kyandar Birrai ce a karin jihohi shida bayan bullar…

Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta ce an samu rahoton bullar kwayar cutar da ake zaton kyandar Birrai ce a karin jihohi shida bayan bullar cutar a jihar Bayelsa a karshen watan da ya gabata.
Rahoton baya-bayan nan na bullar cutar ya nuna an samu bullar cutar har sau 31 a jihohi bakwai na kasar wadanda  suka hada da jihar Bayelsa da Ribas da Ekiti da Akwa Ibom da Legas da kuma Kuros Riba.
Shugaban Cibiyar Yaki da Cututtuka, Chikwe Ihekweazu ya ce “ kawo yanzu ba a samu rahoton mutuwa ba”.
“Ta yi wu bullar cutar da aka samu a karin jihohin ba su da dangantaka da cutar kyandar Birrai amma dai muna ci gaba da bincike”. Inji shi.