Mutum tara sun rasu a sakamakon kamuwa da cutar kwalara mai sa amai da gudawa a Jihar Yobe.
Hukumomin lafiya a jihar sun kuma gano akalla mutane 132 da ke ɗauke da cutar a wasu ƙananan biyar.
Da yake sanarwa a ranar Alhamis, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Lawan Gana, ya bayyana zuwa yanzu, an sallami majinyata 112 da aka tabbatar sun samu sauki.
“Ya zuwa yanzu an tabbatar da ɓullar cutar kwalara a kananan hukumomin Gujba, Fune, Machina, Nangere da Nguru,” in ji kwamishinan lafiyan.
- Yara 50m ke gararamba a titunan Najeriya —Gwamnati
- NNPP na shirin amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi a zaɓen Kano —APC
Ya yi zargi jinkirin kai rahoto ga cibiyoyin kiwon lafiya a matsayin babban abin da ke haddasa mace-macen.
A cewarsa, gwamnatin jihar na yi bakin ƙoƙarinta wajen daƙile wannan matsala.
Amma ya koka bisa yadda jihar ta samu ƙaruwar masu fama da cutar gudawa a sakamakon ruwan sama mai yawa da ambaliyar da aka samu a sassan jihar.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga dukkan abokan hulɗa kan harkar lafiya da shugabannin addini da na gargajiya da kuma ’yan jihar da su haɗa kai da ma’aikatar lafiya da sauran hukumomin da ke da alaƙa da kiwon lafiya domin daƙile yaduwar cutar ta kwalara.