Gwamnonin Arewa Maso Yamma da Arewa maso Tsakiya sun bayyana aniyarsu na rufe makarantu da ke yankin na kwanaki 30 domin dakile yaduwar cutar Kurona a yankin.
Gwamnonin sun ce za a rufe makarantun ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.
Wannan mataki da gwamnonin suka dauka ya biyo bayan kasidar bayan taron da suka yi ne a jihar Kaduna wanda shugaban Kungiyar Gwamnoni ta Arewa maso Yamma, Aminu Masari da shugaban Gwamnonin Arewa ta tsakiya Sani Bello, suka rattaba hannu kuma aka rabawa manema labarai a jihar.
Jihohin tara sun hada da: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Neja, Sakkwato, da Zamfara.
Sun ce, gwamnonin za su dauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumar gudanar da jarabawa ta kasa.