✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: Ana farautar mutanen da suka san wanda ya shigo da ita Najeriya

Gwamnatin jihar Legas ta dukufa wajen neman daukacin mutanen da su kayi mu’amala ta kud da kud da mutumin nan dan kasar Italiya da ya…

Gwamnatin jihar Legas ta dukufa wajen neman daukacin mutanen da su kayi mu’amala ta kud da kud da mutumin nan dan kasar Italiya da ya shiga jihar da cutar Kurona.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Farfesa Akin Abayomi, ya shaida cewa gwamnatin jihar na neman daukacin mutanen da suka yi mu’amala da mutumin tun daga lokacin shigowarsa Najeriya.

Ya ce, mafi yawancin mutanen da ke kamuwa da cutar kan fuskanci matsalar rashin lafiya na dan karamin lokaci sannan su warke, amma cutar ta Kurona tafi kamari da yin lahani ga wadanda suka manyanta.

“Jihar Legas na aiki tukuru tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen kare yaduwar cutar, bisa jagorancin cibiyar kare cututtuka masu yaduwa ta kasa.

Dan Italiyan da ya shigo da cutar ya zo Najeriya domin huldar kasuwancin na kankanin lokaci a ranar Talata da ta gabata daga birnin Milan na kasar Iyaliya.

Cutar ta kwantar da shi kwana guda da shigowarsa inda aka garzaya da shi dakin kebe majinyattan cututtuka masu yaduwa na jihar, kuma aka tabbatar yana dauke da cutar bayan gwajin da aka yi masa a asibitin koyarwa na jami’ar Legas ya tabbatar da yana dauke cutar Kurona ta COVID-19

Kwamishinan kiwon lafiya na Legas ya shaida cewa dan kasar Italiya baya cikin mawuyacin hali.