✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: An killace ‘yan China uku a jihar Filato

Ma’aikatar lafiya a jihar Filato Najeriya ta tabbatar da killace wasu ‘yan kasar China uku saboda fargabar yaduwar cutar Kurona. An dai killace su ne…

Ma’aikatar lafiya a jihar Filato Najeriya ta tabbatar da killace wasu ‘yan kasar China uku saboda fargabar yaduwar cutar Kurona.

An dai killace su ne a yankin Karamar Hukumar Wase ta jihar, Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Nimkong Ndam, ne ya tabbatar da hakan ranar Asabar.

‘Yan kasar China da aka killace na aiki ne da kamfanin hakar ma’adanai a garin Wase.

Kwamishinan, y ace wadanda aka killace sun dawo ne jihar ranar Juma’a Ethiopia, don ci gaba da aikin sun a hakar ma’adanai.

A yanzu haka an kebe su ne a wata cibiyar lafiya don yin bincike.