✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: Allah Ya sa kada ta hana Aikin Hajji!

A halin yanzu dai batun cutar Kurona shi ne ya mamaye ko’ina a fadin duniyar nan ta yadda hankalin al’umma ya karkata gaba daya game…

A halin yanzu dai batun cutar Kurona shi ne ya mamaye ko’ina a fadin duniyar nan ta yadda hankalin al’umma ya karkata gaba daya game da wannan annobar da ta taso tana kokarin mamaye duniya.

Saboda tsoron yaduwar cutar Kurona ne ya sanya hukumomin Saudiyya bayar da sanarwar dakatar da zuwa Umura a kasar tare da kai ziyara garurruwan Makka da Madina har sai abin da hali ya yi.

Bayan hukumomin Saudiyya sun bayar da wannan sanarwar sai kuma kwatsam aka samu rahoton samun wani dan kasar Saudiyya da ya kamu da cutar ta Kurona bayan ya dawo daga kasar Bahrain.

A halin yanzu dai wannan cuta ta Kurona wadda ta samo asali daga kasar China, ta watsu a kasashe fiye da sittin, kuma a kullum yawan kasashen da cutar ke shiga sai karuwa suke yi.

Fargabar da ake yi ita ce, tunda har kasar Saudiyya ta dakatar da zuwa Umura, akwai yiwuwar idan ba a shawo kan matsalar kafin lokacin Aikin Hajji ba za a dakatar da zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin bana, domin ita wannan muguwar cutar mai saurin kisa, ta hanyar cakuduwar jama’a take yaduwa, saboda da zarar an yi cudanya da wanda cutar ta shafa ana iya kamuwa da ita.

Saboda haka hukumomin kasar Saudiyya suka dauki matakin dakatar da zuwa Umara don kada a yada cutar sakamakon cinkoson mutane da za a samu, musamman da yake watan azumin Ramadan ya gabato, wanda lokaci ne da aka fi zuwa aikin Umara a kasar ta Saudiyya.

Sai dai kuma duk yawan mutanen da ake samu a lokacin Umara bai kai na Aikin Hajji ba, domin shi sau daya ake yi a shekara, saboda haka miliyoyin mutane ke taruwa a lokaci guda domin gudanar da wannan muhimmin ibada, amma Umara da yake a kowane lokaci a shekara ana iya yi, bai tara mutane masu dimbin yawa kamar Aikin Hajji, sai dai an fi samun yawan jama’a a lokacin watan Ramadan.

Wannan muguwar cutar ta Kurona ta tsorata mutane, ta sanya ana jin tsoron gaisawa hannu da hannu, yanzu wadansu da kafa suke musabaha saboda tsoron kamuwa da cutar. Kuma ana tsoron haduwa a wuraren ibada da kasuwanni da tashoshin mota da jiragen kasa da kuma musamman tashoshin jiragen sama, inda ta nan ne aka fi shigo da cutar.

A sakamakon bullar wannan cuta harkokin kasuwanci sun fara raguwa saboda mutane suna jin tsoron zirga-zirga a tsakanin kasashen duniya. Kasar China ita cutar ta fara yi wa illa ga tattalin arziki, domin yanzu ana tsoron zuwa kasar, kuma idan an ga dan kasar a wata kasa ana tsoron hulda da shi.

Ita ma kasar Saudiyya ba karamar asarar kudin shiga za ta yi a sakamakon dakatar da Umara da ta yi ba, domin hukumar kasar da mutanenta duk suna amfana da ziyarar da ake kaiwa kasar. Amma yanzu ga wata cuta ta bullo da za ta cutar da tattalin arzikin kasar da na duniya baki daya.

A nan Najeriya kuma cutar ta zama wani kari ne ga masifun da al’ummar kasar ke fama da su wadanda suka takura mutane, suka hana su sakin jiki su fita domin gudanar harkokin arziki. Ina nufin bala’o’i irin su Boko Haram da satar shanu da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da masu kashe mutane haka kawai, yanzu kuma ga cutar Kurona, wadda cuta ce mai hana mu’amala, ta shigo sahu. Allah dai Ya kawo mana sauki.

Idan ba a manta ba, a 1996 kasar Saudiyya ta taba dakatar da wadansu maniyyata daga Najeriya daga gudanar da Aikin Hajji saboda gudun kada su yada cutar sankarau a lokacin Aikin Hajji. Shi ya sanya muke addu’a Allah Ya kawo karshen wannan cuta kafin lokacin Aikin Hajji, domin zai yi wahala hukumomin Saudiyya su yarda a gudanar da wannan muhimmin ibada matukar wannan cuta ta ci gaba da yaduwa, saboda miliyoyin  mutane ne daga kasashen duniya za su hadu a wuri guda a lokaci guda.

Muna fata Allah Ya kiyaye kada a dakatar da Aikin Hajji ga al’ummar  duniya  a karo na farko a tarihin Aikin Hajji.

Allah Ya taimaka a shawo kan wannan muguwar cutar cikin hanzari kafin ta yi wa kasashen duniya sakiyar da ba ruwa.