✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Ebola ta sake bulla a Dimokuradiyyar Kongo

Hakan ma zuwa me wata hudu bayan kawo karshen cutar a kasar

Jamhuriyar Dimokyradiyyar Kongo ta tabbatar da sake bullar zazzabin Ebola a cikinta, wata hudu bayan kawo karshen barkewar cutar a kasar.

Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya ta Kasar ce ta sanar da bullar cutar a ranar Asabar, inda ta cevan gano wani matashi mai shekara 31 a birnin Mbandaka, babban birnin Gudumar Equateur na Kongo, dauke da cutar.

Alamun mara lafiyar sun fara ne a ranar biyar ga Afrilu, amma bai nemi magani ba fiye da mako guda.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an kwantar da shi a Cibiyar Kula da Masu Cutar Ebola a ranar 21 ga watan Afrilun, kuma ya rasu a wannan rana.

“Ba mu da lokacin kanmu,” inji, Daraktan Yankin Afirka na  WHO, Dokta Matshidiso Moeti.

Moeti ya ce, “Cutar ta fara sama da makonni biyu kuma a yanzu muna kokarin dakileta.”

WHO ta ce tuni aka fara kokarin shawo kan cutar a Mbandaka – Cibiyar hada-hadar kasuwanci da ke gabar kogin Kongo inda mutane ke zaune a kusa da juna.

Birnin yana da hanyoyin mota da ruwa da kuma jiragen sama zuwa Babban Birnin Kasar, Kinshasa.   Kongo ta samu bullar cutar Ebola sau 13 a baya, kuma birnin Mbandaka na cikin wanda cutar ta bulla sau biyu  a cikin shekarun 2018 da 2020.

Cutar Ebola da ta barke a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020, a gabashin Kasar, ta kashe kusan mutum 2,300, wanda shi ne adadi na biyu mafi yawa da aka samu a tarihin zazzabin cutar.

Barkewar cutar ta karshe, ita ce wanda aka samu a gabashin kasar, ta kama mutum 11 tsakanin Oktoba zuwa Disamba, sannan ta kashe shida daga cikinsu.