Jamhuriyar Dimokyradiyyar Kongo ta tabbatar da sake bullar zazzabin Ebola a cikinta, wata hudu bayan kawo karshen barkewar cutar a kasar.
Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya ta Kasar ce ta sanar da bullar cutar a ranar Asabar, inda ta cevan gano wani matashi mai shekara 31 a birnin Mbandaka, babban birnin Gudumar Equateur na Kongo, dauke da cutar.
Alamun mara lafiyar sun fara ne a ranar biyar ga Afrilu, amma bai nemi magani ba fiye da mako guda.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an kwantar da shi a Cibiyar Kula da Masu Cutar Ebola a ranar 21 ga watan Afrilun, kuma ya rasu a wannan rana.
“Ba mu da lokacin kanmu,” inji, Daraktan Yankin Afirka na WHO, Dokta Matshidiso Moeti.
Moeti ya ce, “Cutar ta fara sama da makonni biyu kuma a yanzu muna kokarin dakileta.”
WHO ta ce tuni aka fara kokarin shawo kan cutar a Mbandaka – Cibiyar hada-hadar kasuwanci da ke gabar kogin Kongo inda mutane ke zaune a kusa da juna.
Birnin yana da hanyoyin mota da ruwa da kuma jiragen sama zuwa Babban Birnin Kasar, Kinshasa. Kongo ta samu bullar cutar Ebola sau 13 a baya, kuma birnin Mbandaka na cikin wanda cutar ta bulla sau biyu a cikin shekarun 2018 da 2020.
Cutar Ebola da ta barke a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020, a gabashin Kasar, ta kashe kusan mutum 2,300, wanda shi ne adadi na biyu mafi yawa da aka samu a tarihin zazzabin cutar.
Barkewar cutar ta karshe, ita ce wanda aka samu a gabashin kasar, ta kama mutum 11 tsakanin Oktoba zuwa Disamba, sannan ta kashe shida daga cikinsu.