✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Bakon Dauro na kashe yara a kauyen Kaduna

Mazauna kauyen Wusar da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun koka kan yadda cutar Bakon Dauro ta yi sanadiyyar mutuwar yara masu yawa…

Mazauna kauyen Wusar da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun koka kan yadda cutar Bakon Dauro ta yi sanadiyyar mutuwar yara masu yawa a garin a cikin wata biyu.

Dagacin Garin Alhassan Hamidu, ya ce cutar ta faro ne a watan Mayu zuwa watan Yuli, inda a kullum take kashe yara ’yan kasa da shekara biyu zuwa uku da haihuwa.

Ya bayyana wa Aminiya cewa akwai bukatar a kai musu dauki domin ba su da asibiti a kauyen kuma yaransu suna mutuwa.

“Maganar da muke yi da kai sai da aka binne yara uku a ranar Lahadin da ta gabata kuma haka ake yi tun lokacin da annobar ta fado garin Wusar. Yanzu haka muna ganin ta kashe yara kusan 100 a cikin wata biyu,” in ji shi.

Alhaji Murtala Al’usari daya daga cikin iyayen da suka rasa ’ya’yansu a garin ya ce yaran suna farawa ne da zafin jiki daga bisani sai su barke da zawo.

“Yanzu haka ’yata Zainab ta rasu kuma haka ake yi kullum sai kashe yara cutar ke yi har mun soma tunanin ko wata cutar ce daban ba Bakon Dauro ba. Don haka muna kira ga gwamnati ta kawo mana dauki,” inji shi.

Aminiya ta samu ganawa da wadansu mata da suka rasa ’ya’yansu sanadiyar wannan annoba da ta bulla a garin.

Halima Alhaji Ahmadu ta ce ta rasa ’ya’ya biyu a annobar kuma ta ce sun rasu ne ’yan kwanaki da kamuwarsu.

“Ya’ya biyu muka rasa kuma sun kamu da cutar ce da ta barke a wannan gari namu. Sun fara da zafin jiki daga bisani suka barke da zawo. Gaskiya maganin gargajiya na tsassake muke ba su sai dai idan sun barke da zawo sai a nemo na Bature. Muna neman taimako daga gwamnati domin yara mutuwa suke yi,” inji ta.

Ita ma Halira Mahmud wacce ta rasa danta mako uku bayan kishiyarta ta rasa nata ’yar ta ce akwai damuwa a kauyen saboda yawan mutuwa da yara kanana ke yi.

“Wannan abu ya zama annoba matuka domin yara sai kamuwa suke yi kuma suna mutuwa. Ni ma na rasa dana mako uku bayan rasuwar ’yar kishiyata. Saboda haka muna matukar neman taimakon gwamnati domin babu asibiti a nan kauyen,” inji ta.

Goshi Sadamu ita yara biyu ta rasa tare da jikokinta biyu, inda ta ce yaransu bakwai suka kwanta amma hudu sun rasu, uku kuma a yanzu ba su da lafiya.

“Yanzu haka sassake muke ci gaba da nemowa a daji muna ba su tunda dai babu asibiti a wannan kauyen kuma har yanzu cutar sai kama yaran take yi,” inji ta.

Aminiya ta samu labarin cewa asibiti mafi kusa da kauyen Wusar shi ne na garin Kujama mai kimanin tazarar kilomita 17 wanda hakan ya sa akasarin mazauna Wusar ba su iya zuwa asibiti domin neman magani.

Daraktan Sashen Lafiya a Matakin Farko a Hukumar Lafiya ta Jihar Kaduna, Dokta Ado Zakari ya tabbatar da bullar cutar sai dai a cewarsa ya san yaran da suka rasu ba su kai yawan da mutanen suka ambata ba.

Ya ce tuni an aika tura ma’aikata zuwa kauyen domin bincikar lamarin. Ya ce akwai matsalar bullar Bakon Dauro a wasu kananan hukumoin jihar amma suna kokarin magance matsalar.