✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cristiano Ronaldo ya murmure

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sifen sun nuna cewa shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo ya murmure daga raunin da ya…

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sifen sun nuna cewa shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo ya murmure daga raunin da ya samu.
Ronaldo, wanda bai fara yi wa kulob din Real Madrid wasa a kakar wasa ta bana ba, ya samu rauni ne a lokacin da yake buga wa kasar haihuwarsa Fotugal a wasan karshe a gasar cin kofin Nahiyar Turai a tsakanin Fotugal da Faransa a watan Yulin da ya gabata.
Fotugal ce ta samu nasarar lashe kofin a karon farko.
Kamar yadda sanarwar da kulob din Real Madrid ya fitar a ranar Litinin da ta gabata, an nuna tuni Ronaldo ya murmure inda ya ci gaba da yin atisaye da sauran ’yan kwallon.  Ana sa ran Ronaldo zai fara wasansa na farko ga kulob din Madrid ne a gasar La-Liga ta Sifen a tsakanin kulob din da Osasuna a gobe Asabar da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya.
Madrid dai ta samu nasara a wasanni biyu da ta yi a gasar La-Liga ba tare da Ronaldo ba.