✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Za a fara sallamar majinyatan da suka warke a Kano

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa cibiyoyin jinyar wadanda suka harbu…

Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa cibiyoyin jinyar wadanda suka harbu da cutar za su fara sallamar wadanda suka warke.

Nasiru Gawuna ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Alhamis, lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a kan halin da ake ciki dangane da cutar a jihar.

Ya ce gwajin da aka yi wa wasu daga cikin wadanda suka harbu ya nuna cewa sun warke daga cutar amma dole ne a bi ka’idojin da ake bi na sallamar majinyatan,  kafin  su koma ga iyalansu.

Mai kula da tsare-tsare na kwamitin kar ta kwana mai yaki da cutar a jihar, Dokta Tijjani Husseni, ya tabbatar da cewa zuwa yanzu mutane biyar ne suka rasa rayukansu a dalilin cutar a Kano.

Ya kuma bayyana cewa an kammala shirye-shiryen kafa cibiyar gwaje-gwaje ta tafi-da-gidanka saboda inganta aikin gwaje-gwaje a jihar.

Dokta Tijjani Husseni ya ce  yadda ake nuna kyama ga  wadanda suka kamu da cutar yana kawo cikas a  aikin dakile ta,  inda ya bukaci a cigaba da wayar wa al’umma kai.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamiti na musamman mai dauke da kwararru don su taimaka a dakile yaduwar cutar a jihar Kano.