✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Za a ci tarar kamfanonin jiragen sama N1m

NCAA ta ce duk wani kamfanin jiragen sama da ya saba sababbin ka’idojin COVID-19 N1,438,745, a kan ko wanne fasinja

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta yi gargadin cewa duk kamfanin jiragen sama da ya saba sababbin ka’idojin COVID-19 game da killace matafiya zai biya tarar $3,500, kwatankwacin N1,438,745, a kan ko wanne fasinja.

Darakta Janar na Hukumar, Kyaftin Musa Nuhu, a wata sanarwa da ya aike wa kamfanonin, ya ce akwai kuma yiwuwar haramta wa kamfanin da ya doge wajen saba dokar aiki.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu dokar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa-da-kasa da aka fitar game da killace fasinjojin da ke shigowa Najeriya tana aiki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Kyaftin Nuhu yana karawa da cewa garambawul da aka yi wa dokar ta killace fasinjoji masu shigowa ko masu fita daga Najeriya ya fara aiki ne ranar 5 ga watan Disamba.

Hawa jirgi sai da lakani

Game da fasinjoji na cikin gida kuwa, Kyaftin Nuhu cewa ya yi kada a kuskura a kyale kowa ya hau jirgi sai ya nuna takardar izinin yin haka mai dauke da lakanin ‘QR Code’.

Wannan takardar izini, a cewarsa, ta hada da sakamakon gwajin da ke nuna mutum ba ya dauke da COVID-19 wanda ya yi kasa da sa’a 48 kafin lokacin hawa jirgin.

“Game da fasinjoji masu fita waje kuwa, za a kyale fasinja ya hau jirgi ne kawai ya bar Najeriya idan ya nuna shaidar yin allurar riga-kafin kamuwa da COVID-19.

“In hakan bai samu ba, to fasinja ya nuna shaidar gwajin COVID-19 da aka yi masa kasa da sa’a 48 kafin lokacin tafiya.

“Duk kamfanin da ya saba wadannan ka’idoji zai biya tarar Dala 3,500 a kan ko wanne fasinja.

“Su kuwa kamfanonin da suke saba wannan ka’ida a-kai-a-kai, to za su biya tarar Dala 3,500 a kan ko wanne fasinja”, inji shi.

%d bloggers like this: