Kusan daukacin titunan da ke Jos, babban birnin jihar Filato, sun kasance fayau ranar Juma’a sakamakon dokar da gwamnati ta kafa ta hana fita kwata-kwata.
Dokar ta tsawon mako guda wadda ta fara aiki da tsakar daren Alhamis na cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka don hana cutar coronavirus shiga balle ta yadu.
Da ya zagaya birnin na Jos da kewaye, wakilin Aminiya ya ga yadda dukkan kasuwanni da tashoshin mota suka kasance a kulle, babu kowa.
Rahotanni daga dukkan kananan hukumomin jihar 17 sun tabbatar da cewa jama’a sun yi biyayya ga wannan doka, ta hanyar zama a gidajensu.
A lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, wani mazaunin garin Bukur da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, kuma shugaban kungiyar mahauta ta Jihar Filato, Alhaji Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa, “Mu mutanen Bukur mun ba da hadin kai ga wannan doka ta hana fita da gwamnatin jihar Filato ta kafa”.
Ya yi kira ga al’ummar Filato su zamanto masu biyayya ga gwamnati, a wannan aiki da aka sanya a gaba, na yaki da wannan annoba da ta addabi duniya.
“Wannan cuta yanzu tana kashe mutane da dama a duniya. Don haka ya kamata jama’a su ba da goyan baya kan dukkan matakan dakile wannan cuta da gwamnati ta dauka domin a sami nasara”.
- COVID-19: ‘Najeriya za ta shiga makwanni 2 mafiya hadari.’
- Hotuna: Yadda dokar hana fita ta kasance a Plateau
Shi ma wani mazaunin Jos babban birnin jihar ta Filato, Alhaji Habibu Abubakar, cewa ya yi sun bi wannan doka sun zauna a gida, kamar yadda gwamnati ta umarta.
“Ba a wannan lokaci ya kamata gwamnati ta kafa wannan doka ba, idan aka dubi halin kuncin rayuwar da talakawan Najeriya suke ciki.
“Mafiya yawan ‘yan Najeriya sai sun fita suke samun abin da za su ciyar da kansu da iyalansu. Don haka, wannan abu akwai takurawa sosai a ciki, musamman ga talakawan Najeriya”, inji shi.
Ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa su sake tunani kan al’amarin hana Sallar Juma’a da hana zuwa coci a ranar Lahadi.
‘’Idan har gwamnan Jihar Rivers zai dage doka kan musulmi su je su yi sallar Juma’a, Kiristoci su je coci a ranar Lahadi, a roki Allah Ya yaye mana wannan annoba, me zai sanya gwamnonin Arewa ba za su dauki irin wannan mataki ba?’’