✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta kashe likitoci 303 a Indonesia

Kungiyar Likitocin Kasar Indonesia ta tabbatar da adadin likitocin da suka mutu.

Akalla likitoci 303 ne suka mutu a kasar Indonesia bayan harbuwa da cutar COVID-19, kamar yadda Kungiyar Likitocin kasar ta bayyana a ranar Alhamis.

Daga cikin adadin, 169 manyan likitoci ne, sai kananan guda 129, sai likitocin masu neman kwarewa guda biyar.

Galibi dai tsofaffin likitocin da suka mutu bayan harbuwa da cutar sun fara ne daga shekaru 81 zuwa 85.

Mafiya karancin shekaru da suka mutu daga cikinsu su ne masu shekaru 28 zuwa 30, su ma kimanin mutane 11.

Watan Janairun 2021 shi ne watan da aka fi samun mace-macen likitocin inda mutum 57 suka mutu, adadin da ya haura wanda aka samu a watan Disambar 2020 mai likitoci 55.

Jerin yankunan da aka fi samun mace-macen sun hada da Java ta Gabas mai mutane 60, Jakarta guda 44, Java ta Tsakiya, 44, Java ta Yamma, 34, da kuma Arewacin Sumatra mai mutane 27.