✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19 ta kama mutum 4,035 a Najeriya

Kawo yanzu wannan shi ne mafi girma na wadanda suka kamu da cutar a rana guda a Najeriya

Akalla mutum 4,035 ne Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta tabbatar a matsayin wadanda suka sake kamuwa da cutar COVID-19 a fadin kasar a ranar Laraba.

NCDC ta sanar da adadin wadanda suka kamun ne a shafinta na intanet a ranar Alhamis.

Daga cikin wuraren da aka samu sabbin wadanda suka kamu, Jihar Lagos ce ke kan gaba da mutum 3,393, sai Ribas mai mutum 260 sannan Edo 62  da Akwa Ibom, 42.

Jihar Kaduna na da 39, Ekiti da Oyo na da 38 kowanensu, Delta da Kano na da 31 kowanensu. Abiya na da 26, Bauchi na da 15, Ondo na da 14, Enugu na da mutum tara, sai Jihar Kwara mai mutum bakwai.

Adadin sabbin wadanda suka kamu da cutar shi ne mafi girma da aka taba samu a rana guda a fadin Najeriya tun bayan bullar cutar a watan Fabrairun 2020.

Daga bullar cutar zuwa yanzu, adadin wadanda suka kamu da ita ya kai 231,413, daga ciki an sallami mutum 211,853 daga cibiyoyin killace mutane.

Adadin wadanda suka rasa rayukansu a sanadin cutar kuma 2,991.