Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya ce a cikin mutum 73 da aka tabbatar sun kamu da coronavirus a jihar, yanzu haka saura takws kacal a cibiyar killace majinyata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Maradun, inda ya je hutun Sallah.
Ya kuma yaba da kwazon ma’aikatan lafiyar jihar wajen tantance da kuma kula da wadanda suka kamu da cutar.
- Yadda aka samu sabanin alkaluma tsakanin NCDC da Zamfara
- Coronavirus: Ana neman wani ‘majinyaci’ ruwa a jallo a Zamfara
“Mun rasa mutum biyar sanadiyyar wannan annoba amma wasu da dama sun warke a cibiyar da aka killace su kuma an sallame su sun koma cikin danginsu.
“Wannan abin a yaba ya faru ne saboda kokarin ma’aikatan lafiyarmu, da kokarinmu na cimma dukkan sharuddan kauce wa kamuwa da kuma hadin kan al’umma wajen kula da ka’idojin kariya.
“Ina so na jaddada cewa COVID-19 gaskiya ce har yanzu kuma tana barna kuma tana da hadari ga rayuwar dan-Adam, don haka dole mu hada hannu mu ci gaba da daukar matakan da ke dakile saurin yaduwar cutar a tsakanin al’umma ta yadda za mu gudu tare, mu tsira tare a yakin da muke yi da annobar”.
Gwaji ba taba juna
Ya yi kira ga jama’a da su yi gwajin cutar a daya daga cikin cibiyoyin da aka kakkafa a daukacin kananan hukumomin jihar 14.
“Kwanan nan gwamnati ta kafa cibiyar daukar samfur wadda ba a taba juna da kuma dakin binciken cutar a Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da keGusau wadda babu irinta a duk kasar nan a yunkurinmu na gano masu dauke da cutar cikin hanzari don ceton rayuwar al’umma.
“Har jihohi makwabta ma cibiyar za ta rika taimaka musu saboda mu shawo yaduwar cutar daga jiha zuwa jiha”, inji shi.
A makon jiya ne dai gwamnatin ta Zamfara ta ce ba ta amince da wasu alkaluma da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar game da adadin wadanda suka kamu ajihar.
Daga bisani dai hukumar ta gyara kurenta ta kuma nemi afuwa.