✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Sama da majinyata 1,000 sun warke a Najeriya

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan sun nuna cewa adadin majinyata 1,180 aka sallama bayan sun warke daga…

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan sun nuna cewa adadin majinyata 1,180 aka sallama bayan sun warke daga cutar coronavirus.

Kididdigar NCDC din ta tsakar daren 14 ga watan Mayu dai ta nuna cewa karin mutum 193 ne suka kamu, lamarin da ya kai jimillar wadanda aka tabbatar zuwa 5,162.

Hukumar ta NCDC ta kuma ce a cikin wannan adadi an rasa mutum 167.

Hakan dai na nufin a yanzu haka akwai mutum 3,815 da ke jinya.

Daga cikin sabbin majinyatan dai 58 a jihar Legas suke, 46 a Kano, 35 a Jigawa, 12 a Yobe, da kuma tara a Yankin Babban Birnin Tarayya.

Sai kuma mutum bakwai  a jihar Ogun, biyar a Gombe da Filato, hudu a Imo, sai Kwara da Borno da Edo  da ke da mutum uku uku.

Jihohin Bauchi, da Nasarawa, da Ondo na da mutum guda ko wacce.

Jihar Legas ce dai ke kan gaba a yawan wadanda aka sallama bayan sun warke daga cutar COVID-19