✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Har yanzu ban warke ba –El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Laraba ya bayyana cewa har yanzu yana killace tun bayan gwajin da aka yi masa yana dauke…

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Laraba ya bayyana cewa har yanzu yana killace tun bayan gwajin da aka yi masa yana dauke da cutar coronavirus  kuma bai warke ba.

Gwamnan ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Laraba.

”Idan na warke daga cutar zan sanar halin da nake ciki, da kaina zan bayyana warkewata daga cutar.“ in ji Gwamnan.

Ya bukaci jama’ar jihar su yi watsi da labaran da ake yadawa cewa ya warke daga cutar da yake da ita.

El-Rufai, a karon farko ya jagoranci zaman tattaunawar da aka yi da aka yi da majalisar zartarwar jihar tun bayan da ya kamu da wannan cuta, kuma idan warke  ya ce zai sanar.

A ranar 28 ga watan Maris 2020 ne sakamakon gwajin da aka yi wa Gwamnan ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus.