Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a ranar Laraba ya bayyana cewa har yanzu yana killace tun bayan gwajin da aka yi masa yana dauke da cutar coronavirus kuma bai warke ba.
Gwamnan ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Laraba.
”Idan na warke daga cutar zan sanar halin da nake ciki, da kaina zan bayyana warkewata daga cutar.“ in ji Gwamnan.
Ya bukaci jama’ar jihar su yi watsi da labaran da ake yadawa cewa ya warke daga cutar da yake da ita.
- Gwamna El-Rufa’i ya kamu da Coronavirus
- Maidakin El-Rufai ba ta kamu da Coronavirus ba
- Dokar Hana Sallar Juma’a: An kama Limamai biyu a Kaduna
El-Rufai, a karon farko ya jagoranci zaman tattaunawar da aka yi da aka yi da majalisar zartarwar jihar tun bayan da ya kamu da wannan cuta, kuma idan warke ya ce zai sanar.
A ranar 28 ga watan Maris 2020 ne sakamakon gwajin da aka yi wa Gwamnan ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus.
KADUNA UPDATE: Earlier Wednesday 10am-2pm, I took few hours during isolation to chair a virtual meeting of the State Executive Council.
I haven’t been cleared of Covid-19 yet & will personally announce when confirmed negative. Ignore all fake news even if you like it.-@elrufai pic.twitter.com/je3QW1oOHM
— Nasir Ahmad El-Rufai (@elrufai) April 15, 2020