Hukumomi a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta cin tarar N20,000 da daurin wata 6, ko kuma duka biyun ga duk wanda bai sanya takunkumi ba, musamman a cikin taron jama’a.
Wannan mataki na daga cikin matakan da gwamnati ke son dauka da nufin kare rayukan ’yan kasa daga cutar coronavirus.
- Karin mutum 324 sun kamu da Coronavirus a Najeriya
- An killace Buratai bayan COVID-19 ta kashe Janar din soja
- Janar din sojojin Najeriya 18 sun kamu da COVID-19
- COVID-19 ta kashe Janar din Sojin Najeriya
Wani jami’in kiwon lafiya a Asibitin Kwararru na Bauchi, Malam Muhammed Bello Dauda, ya ce za a fara daukar matakin cin tarar duk wanda bai sanya takunkumin ba koda bisa kuskure ne.
Ya kuma yi kira ga mutane su rika yin nesa-nesa da juna don kare kai daga cutar da kuma taimakawa wurin dakile yaduwarta.
Jami’in ya yi karin haske da cewa cutar coronavirus ta dawo a karo na biyu a cikin watan Nuwamba inda aka samu mace-mace.
Don haka ya kuma yi kira ga mutane su rika yin nesa-nesa da juna don kare kai daga cutar da kuma taimakawa wurin dakile yaduwarta.
Ya ce an dauki matakin ne da nufin hana yaduwar cutar ta hanyar cudanya da mutane, shiga mot da zarar mutum zai fito ya yi mu’amala da jama’a a kasuwanni da sauran wurare.
A halin da ake ciki, Gidauniyar BUA, mallakar Abdulsamad Isyaka Rabiu ta aika wa Gwamnatin Jihar Bauchi da kyautar motocin daukar marasa lafiya da kuma dubban takunkumin rufe hanci.
Alhaji Idi Hong da ya kawo kayayyakin kana ya wakilcin shugaban gidauniyar wurin ba da kayan, ya ce manufar wannan taimako ita ce rage wa al’umma radadin annobar.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, shi ne ya karbi kayayyakin ya kuma gode wa shugaban gidauniyar BUA, Abdulsamad Isyaka Rabiu tare yi alkawarin amfani da kayayykin ta hanyar da ya kamata.