✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Najeriya ta aminta da rigakafin AstraZeneca da kasashe 13 suka dakatar

Gwamnati ta ce matsalar da rigakafin kan iya haifarwa ba shi girma ga 'yan Najeriya.

Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 na Kasa (PTF), ya ce allurar rigakafin cutar na kamfanin Oxford AstraZeneca ba shi da wata matsala ga ‘yan Najeriya duk da cewar wasu kasashe sun koka kan rashin ingancinsa.

Manajan Lura da Abin da ke Faruwa (NIM) na PTF, Dokta Mukhtar Muhammad, ne ya bayyana haka a taron hadin gwiwar na Kwamitin ranar Litinin.

A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne kasashen Denmark, Norway, Austria, Estonia, Latvia, Lithuania, Iceland, and Luxembourg, suka dakatar da yin allurar kamfanin saboda rashin tabbas.

Dakatarwar na daga cikin shirin gwamnatocin kasashen na kara yin bincike kan inganci da kuma abin da rigakafin na Oxford AstraZeneca ka iya haifarwa.

Har wa yau, kasashe irinsu Jamus, Italiya, Faransa, Spain da Netherlands, na daga cikin wanda su ma suka tsaida yin rigakafin saboda samun barkewar jini ga wanda ake yi wa.

Sai dai Muhammad ya ce matsalar da rigakafin kan iya haifarwa ba shi wani girma ko tasiri ga ‘yan Najeriya.

A cewarsa, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta tabbatar da ingancin allurar a kwanaki uku da suka gabata.

Sannan ya shawarci wanda aka yi wa rigakafin, da suka ji wani yanayi na daban da su garzaya zuwa asibitocin da suka dace don bincikar lafiyarsu.