Annobar coronavirus na ci gaba da kama mutane da dama a Najeriya ciki har da manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa masu rike da sarautun gargajiya da dai sauransu.
Aminiya ta yi nazari tare da zakulo muku muhimman mutane guda bakwai da cutar ta kama a cikin wata dayan da ya gabata.
- COVID-19: An kwaso ‘yan Najeriya 322 da suka makale a Amurka
- Barebari sun fi Fulani kamuwa da COVID-19
—Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu
A ranar 30 ga watan Yuni gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo da ke Kudu-maso-Yammacin Najeriya ya kamu da cutar COVID-19.
Gwamna Akeredolu a cikin wani bidiyo, ya ce sakamakon gwajin cutar da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar COVID-19, kuma zai fara killace kansa, domin likitoci su kula da lafiyarsa.
—Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa
Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa ya kamu da cutar coronavirus.
Okowa ya sanar da kamuwarsa da matarsa da curtar a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar daya ga watan Yuli.
“Ni da mai dakina mun kamu da COVID-19 amma har yanzu da kwarinmu a inda muka killace kanmu”, inji shi.
Kamuwar gwamnan na zuwa ne kwana biyar bayan ya sanar da harbuwar diyarsa wadda ta sa sauran iyalansa suka fara killace kansu.
—Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu
A ranar 8 ga watan Yuni aka sanar da cewa, an killace Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia bayan ya harbu da cutar coronavirus.
Ikpeazu ya killace kansa ne tun bayan fitowar sakamakon gwajin da ya tabbatar da ya kamu da cutar coronavirus, a cewar Kwamishinan Yada Labaran jihar John Okiyi Kalu.
—Tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi
Abiola Ajimobi tsohon Gwamnan Jihar Oyo ya rasu bayan sassan jikinsa da dama sun daina aiki sakamakon kamuwarsa da cutar COVID-19.
Gwamnatin Jihar Legas inda Ajimobi ya rasu, ta ce sassan jikin nasa sun bar aiki ne bayan tsananin da cutar ta COVID-19 ta yi a jikinsa.
A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni 2020, Allah Ya yi wa Ajimobi rasuwa yana da shekaru 70.
—Sanata Sikiru Adebayo Osinowo
Sanata mai wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Sikiru Osinowo ya riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar a ranar 15 ga watan Yuni.
Hukumomin jihar Legas sun ce cutar COVID-19 tayi ajalin sa ne a Asibitin Kwararru da ke Kula da Cututtukan Zuciya, daya daga cikin cibiyoyin killace masu COVID-19 a jihar Legas.
—Dan majalisar jihar Bauchi, Tukur Ibrahim
Dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Toro da Jama’are a Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Tukur Ibrahim ya kamu da cutar coronavirus.
Kakakin Majalisar Abubakar Sulaiman ya bayyana hakan yayin zamansu na musamman a ranar Litinin bayan dawowarsu daga hutu.