Majalisar Dokokin Jihar Kano ta jingine dawowa zamanta a wani yunkuri na yi wa gwamnatin jihar biyayya wacce ta nemi ma’aikata su zauna a gida.
Shugaban Majalisar, Hamisu Ibrahim-Chidari ne ya bayar da sanarwar dage komawar zauren a wata takarda da daraktan yada labaran majalisar Uba Abdullahi ya raba wa manema labarai a cikin birnin Dabo a ranar Juma’a.
- Yadda sunan ‘Corona’ ya janyo wa wata Mata tsangwama
- Ma’aikatan Jami’a sun sa ranar gurgunta harkokin Ilimi a Najeriya
- An gurfanar da masu gyara a kotu kan zargin satar mota
A baya dai Majalisar ta ayyana ranar 25, ga watan Janairu a matsayin ranar dawo da ci gaban da zamanta, inda a yanzu ta jingine dawowar domin yi wa umarnin Gwamnatin Jihar biyayya da manufar dakile yaduwar cutar Coronavirus.
Ibrahim-Chidari, ya ce ’yan majalisar za su bi umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na zama a gida, don marawa gwamnatin baya kan kudurinta na dakile yaduwar cutar COVID-19.
“Na tabbata gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Ganduje na iya bakin kokarinta na ganin ta dakile yaduwar cutar COVID-19 a fadin Jihar.
“Gwamnatin ta cancanci a jinjina mata kan tsare-tsarenta da take yi da shirya taruka da masu ruwa da tsaki a fadin jihar domin wayar da kan al’umma dangane da matakan kariya da suka dace a kiyaye.”
“Cutar ta dawo, muna bukatar kowa ya bayar da tasa gudunmawar musmnman shugabannin addini da su ci gaba da addu’o’in ganin an kawo karshen wannan annobar a Jihar da kasa baki daya,” In ji shi.
Shugaban Majalisar ya bukaci mazauna Kano da su dabi’antu da kiyaye dokokin kariya na dakile yaduwar COVID-19 kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta sannan su karfafi gwiwar gwamnati wajen yaki da cutar.
Ana iya tuna cewa kwanaki kadan da suka gabata ne gwamnatin jihar ta ba dukkan ma’aikatan jihar zama a gida har zuwa lokacin da za a fidda wata sabuwar sanarwar.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, gwamnatin jihar ta ce sanarwar zaman gidan ba ta shafi malamai da ma’aikatn makarantun ba, don haka za su ci gaba da zuwa aiki kamar yadda suka saba.