✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Jigawa ta killace almajirai sama da 30,000

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce yanzu haka akwai almajirai 30,000 da ta killace a kananan hukumomi biyar. Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ne ya…

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce yanzu haka akwai almajirai 30,000 da ta killace a kananan hukumomi biyar.

Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana haka a lokacin da tawagar gwamantin tarayya da aka tura jihar Kano ta tallafa a yaki annobar coronavirus ta kai mishi ziyara.

Gwamnan ya ce almajirai dubu bakwai a ko wacce daga cikin kananan hukumomin biyar wadanda gwamnatinsa ke kula da su kuma galibinsu ba ’yan asalin jihar ba ne.

Tun da farko da yake jawabi, shugaban tawagar ta gwamnatin tarayya, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, ya ce ya gamsu da matakan da gwamnatin Jigawa ke dauka na yaki da annobar, musamman yadda ta killace almajiran, da tsarin bai wa wadanda bas a dauke da COVID-19 N10,000 da sabon dinki kafin mayar da su gaban iyayensu.

Sai dai masanin kiwon lafiyar ya tausaya da yadda almajiran suka shiga kunci saboda rashin ganin mahaifansu.

Ya kuma bukaci gwamnatin ta sanya kayan kallo a dakunan da almajiran suke saboda hakan zai debe masu kewa a zaman da suke yi na kadaici.

Gwamnatin ta jigawa dai ta bukaci tawagar da ta taimaka wa Jahar ta yadda za ta yi nasara wajan yakar annobar ta coronavirus.