Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bukaci a baiwa jama’a damar yin walwala a jihohinsu, amma banda yin abin da ya shafi taron jama’a.
Wannan bukata ta gwamnonin na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin kwanaki 14 na biyu na dokar zaman gida da gwamnatin tarayya ta ayyana wasu yankunan kasar ke karewa a daren Litinin.
Yankunan da aka ayyana dokar dai su ne jihohin Legas da Yankin Babban birnin Tarayya. Jihar Ogun ta jinkirta fara aiwatar da dokar lokaci guda da sauran yankunan.
Gwamnonin sun bayyana wannan bukatar ne ranar Asabar a wata wasika da suka aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Cika-Aiki a Kan Yaki da Covid-19 na Kasa Boss Mustapha.
A maimakon dokar hana fitar, kungiyar gwamnonin ta bukaci a kafa dokar tilasta wa jama’a amfani da takunkumin fuska na kariya daga annobar a lokacin da suka fito waje.
Wasikar, wacce ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, an rubuta ta ne a matsayin matakin bibiyar taro ta wayar salula da gwamnonin suka yi da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo a ranar 22 ga watan Afrilu.
Shawarwarin da gwamnonin suka bayar a wasikar sun hada da hana zirga-zirga daga jiha zuwa wata, sai dai in kayan abinci, da magani, da kayan gona, da albarkatun man fetur, za a kai; da kafa dokar hana fita da daddare da hana zirga-zirgar jiragen sama.
Gwamnonin sun kuma bukaci shiga tsarin da zai ba su damar daukar mataki na bai daya na dakile annobar.
Zuwa yanzu dai alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar sun nuna cewa mutanen da suka kamu da Codi-19 a Najeriya sun haura 1,000.