Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ya ce Gwamnatin Tarayya za ta binciki zargin karya ka’idojin COVID-19 a filayen jiragen saman kasar nan guda uku.
Ya ce, “Idan aka same su da laifi, wadanda ake zargin za su iya fuskantar hukuncin daurin watanni biyu zuwa shekara goma ko tara ko kuma duka biyun”.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin jawabin kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar a Abuja.
Hukumar Dake Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta zargi gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari da karya ka’idojin, ko da dai dukkansu sun musanta zargin.
Hadi Sirika ya ce amma idan bincike ya tabbatar ba su karya dokokin ba, to za a nemi gafarar su.
Ya ce, “FAAN ta kai kara kan abun da ya faru.
“Wadanda ake zargin sun hada da tsohon gwamnan Zamfara wanda ko a ranar Laraba sai da na yi magana da shi mai tsawo sai kuma gwamnan Adamawa mai ci, Ahmadu Fintiri.
“Abdul’aziz Yari dai ya je Kano ranar Asabar, Fintiri kuma Fatakwal yayin da Cif Nduka Obaigbena shi kuma a Abuja aka zarge shi da karya dokar.
“Yanzu haka muna nan mun dukufa bincike, in mun same su da laifi, za mu dauki matakin da ya dace, idan kuma ba su da laifi, to za mu nemi afuwarsu.
“Ina kira ga manyan mutane da su nuna dattaku a matsayinsu na manya ta hanyar ci gaba da bin dokar”, inji ministan.