Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen da suka ci gaba da su bunkasa yadda ake raba maganin rigakafin cutar Coronavirus domin ganin nahiyar Afirka da sauran kasashe masu tasowa sun samu.
Yayin da yake jawabi wajen taron Tsaro da Zaman Lafiya na Duniya da ke gudana a Paris a karkashin jagorancin Shugaba Emmanuel Macron, Buhari ya ce adadin mutanen da aka yiwa allurar rigakafin a Afirka da wadanda aka yiwa a nahiyar Turai ya nuna yadda aka fi fifita bangare guda.
Shugaban Najeriya ya ce ya zama wajibi a samu daidaito wajen tsari da kuma yadda ake raba allurar rigakafin ga kasashen duniya, domin abinda ake gani yanzu yana nuna rashin daidato da kuma gamsuwa da tsarin.
A taron wanda ya samu halartar Mataimakiyar Shugabar Amurka Kamala Harris, Buhari ya ce alkaluman da ake da su na nuna cewar jama’a kadan ne suka karbi rigakafin a nahiyar Afirka, yayin da wasu kuma a kasashen duniya har sun fara ba da zagaye na 3 na rigakafin, musamman kasashen da suka ci gaba.
Buhari ya ce gibin da ake samu wajen yi wa jama’ar Afirka allurar rigakafin na zagon kasa wajen yaki da cutar, abinda ya bayyana shi a matsayin babbar koma baya ga nahiyar da kuma duniya baki daya.
Buhari ya ce muddin aka amince cewar yin rigakafin itace babbar hanyar dakile cutar, toh ya zama wajibi masu ruwa da tsaki a harkar yaki da cutar su tashi tsaye wajen cike gibin samun maganin a nahiyar Afirka.
Ya kuma yaba wa Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda gwamnatinsa ta bai wa Afirka kyautar allura miliyan 10 domin yi wa jama’a rigakafi, ya ce wadata nahiyar da maganin ne kawai zai taimaka wajen shawo kan cutar.