Shugaban Kula da Gidan Gyaran Tarbiyya (Kurkuku) na garin Kafanchan, Cif Sufuritanda Mathias Dzuzu, ya tabbatar da sakin mutum uku daga gidan yarin bisa umurnin da Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa’i ya bayar.
Shugaban ya shaidawa manema labarai a gidan yarin ranar Alhamis bayan ziyarar da Alqalin Kotun Babban Kotun Kafanchan (Higher Court) na Kafanchan ya kai gidan yarin.
Dzuzu, ya ce mutum ukun da aka sallama su ne wadanda suka haura shekara 60 a duniya kuma suke fama da matsalar rashin lafiya sannan watanni kadan ya rage su kammala zaman gidan kason.
Ya ce, baya ga mutum ukun da gwamnatin jihar ta sallama, shi ma Alqalin Babban Kotun na Kafanchan, Samuel Daka ya bayar da belin wasu mutum shida bayan ya duba lamarinsu.
- COVID-19: An killace mutum biyu a asibitin Kafanchan
- Kungiyoyi sun ziyarci kurkuku da asibitin Kafanchan
Ya kara da cewa, a halin yanzu gidan Gyara Halinka na Kafanchan mai cin mutum 220 yana dauke da mutum 100 ne.
“Tun farko an tsara gidan yarin zai dauki mutane 110 ne amma daga baya bayan aiwatar da wasu gyare-gyare sai ya koma daukar mutum 220, amma a halin yanzu mutane 100 ne a ciki.” In ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya bayar da umarnin sallamar mutum 72 a gidajen kurkukun jihar bisa umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na rage cunkoso a gidajen yari saboda matsalar cutar COVID-19.