✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Yawan masu cutar a Najeriya ya doshi 3,000

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Talata an samu mutum 148 da aka tabbatar sun kamu…

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Talata an samu mutum 148 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus.

Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa, “Zuwa karfe 11.40 na daren 5 ga watan Mayu, mutum 2,950 ne aka tabbatar da sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Daga cikin wadannan mutum 148 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan dai, 43 a jihar Legas suke, sai 32 a Kano, 14 a Zamfara, 10 a Yankin Babban Birnin Tarayya.

Akwai kuma tara a Katsina, bakwai a Taraba, shida a Borno da Ogun, sai biyar a jihar Oyo.

Jihohin Bauchi da Kaduna da Edo na da mutum uku uku, sai Adamawa da Gombe da suke da mutum biyu biyu da kuma jihohin Sakkwato, da Kebbi da Plateau da ke da mutum daya daya da suka kamu.

Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 481 bayan sun samu sauki, yayin da mutum 98 suka riga mu gidan gaskiya.

Kididdigar da hukumar NCDC ta fitar ta nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar ya doshi 3,000, yayin da wadanda suka rasu a sakamakon cutar suka tasan ma 100 a Najeriya.