✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude sabuwar cibiyar killace masu Coronavirus a Legas

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da cibiyar killace masu cutar Covid-19 mai gadaje 80 da ke Oniru a jihar. Gwamnan ne ya shaida hakan…

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da cibiyar killace masu cutar Covid-19 mai gadaje 80 da ke Oniru a jihar.

Gwamnan ne ya shaida hakan a kafafen sada zumuntarsa.

Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa za su ci gaba da fadada cibiyoyin killace masu cutar a daidai lokacin da suke cin galaba a yaki da yaduwar annobar.

Ya ce, sun fadada cibiyoyin gwajin cutar zuwa kusa da jama’a kamar yadda yake a cikin tsarin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC).

Zuwa yanzu jihar Legas ce a kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da coronavirus a Najeriya inda take da yawan wadanda suka kamu mutum 430 cikin mutum 782 da suka kamu a Najeriya.

Wani sashe na sabuwar cibiyar killace masu coronavirus ta Oniru a Legas

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Daga tsakiya a can kuryar, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu tare da jami’an kiwon lafiya a sabuwar cibiyar killace masu coronavirus ta Oniru a Legas