✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Yawan wadanda suka kamu ya karu da 11

Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 11. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC),…

Yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 11.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), wadda ta bayar da snarwar hakan a shafinta na Twitter, ta ce an samu mutanen 11 ne a jihar Legas.

“Zuwa karfe 11.00 na daren 14 ga watan Afrilu, an samu mutum 373 da aka tabbatar sun kamu da #COVID-19 a Najeriya—99 daga cikinsu an sallame su, yayin da 11 kuma suka riga mu gidan gaskiya.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da mutum 214, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke bi mata da mutum 58.

Tun bayan da aka samu mutum na farko a Kano ne dai adadin jihohin da ke da wadanda aka tabbatar sun kamu ya kai 20 ciki har da Yankin Babban Birnin Tarayya.