Rundunar ‘yan sandan Legas ta gurfanar da wasu mutum 202 da ake tuhuma da karya dokar zama a gida a kokarin gwamnati na hana yaɗuwar annobar Coronavirus.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa wadanda ake zargin an kama wasunsu nayin kwallon kafa ne a manyan titunan jihar yayin da aka kama wasu a lokacin da suke motsa jini a cikin ayari lamarin da ya saba dokar nan ta nisantar juna inda aka gurfanar dasu a kotun tafi-da-gidanka a ranar Alhamis.
Ya ce, an tuhume su da saba dokar bada tazara na gwamnatin jihar Legas lamarin da ya saba dokar kiyaye yaɗuwar cututtukan na gwamnatin Legas ta shekarar 2020, sashin dokar 8(1) ( a) da (b) da 17(1) (i).
“Laifi ne da za a iya hukunta su a karkashin dokar mai lamba 58 P16 ta lafiyar al’umma, dokar gwamnatin jihar Legas ta shekarar 2015.”
Bala Elkana, ya ce mutum 189 cikin wadanda aka gurfanar sun amsa laifinsu yayin da 13 daga cikinsu basu amsa laifin da aka tuhume su ba, ” Kotun ta same su da laifin inda aka yanke masu biyan tarar Naira dubu 10 kowannensu tare da yi wa kasa hidima na tsawon sa’a biyu.” In ji shi.
Ya kara da cewa wadanda aka gurfanar masu shekaru 15 zuwa 41 an kama su ne a unguwannin da suka hada da: Iju da Sabo da Ikeja da Itire da Ikotun da Ogudu da Akinpelu da Maroko da Alapere da Anthony da Orile da Owode Onirin da yankin Ilemba Hausa.