An samu karin mutum 117 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya—adadin da ya zarta duk wanda aka samu a baya wajen karuwa a cikin sa’o’i 24.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ce ta wallafa alkaluman a shafinta na Twitter.
Hamsin da tara daga cikin wannan adadi, inji hukumar, mazauna jihar Legas ne, yayin da 29 ke zaune a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Sauran wuraren da aka tabbatar da samun wadanda suka kamu su ne Kano mai mutum 14, da Borno mai mutum shida, da Katsina mai mutum hudu, da Ogun mai mutum uku.
Su kuma jihohin Bauci da Ribas ko wacce na da mutum guda.
“Zuwa karfe 11.25 na daren 21 ga watan Afrilu, wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya mutum 782 ne”, inji NCDC, wadda ta kara da cewa an sallami 197 daga cikinsu yayin da 25 suka riga mu gidan gaskiya.
A yanzu dai adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu a jihar Legas ya kai 430, na Abuja 118, na Kano kuma 73.
Har zuwa farkon watan Afrilu dai babu wanda aka tabbatar ya kamu da cutar a jihar Kano, amma tun daga lokacin adadin yake ta karuwa ba kakkautawa.