Uban jam’iyyar APC Cif Ahmad Bola Tinubu ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 200 domin yakar annobar cutar coronavirus.
Cif Tinubu ya ce zai bai wa gwamnatin Jihar Legas Naira miliyan 100 yayin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) za ta samu Naira miliyan 100.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne a wata takardar sakon bikin cikar sa shekaru 68 a duniya wacce ya sanya wa hannu, yana cewa annobar cutar ta sanya ya janye da dama daga cikin ayyukan da ya shirya yi a bana domin guje wa taron jama’a, sannan ya sha alwashin yin tarurrukan a badi.
“Wannan annoba ta hana mu taruwa mu yi bikin murnar cika ta shekaru 68 a duniya, amma duk da haka zan yi murnar ta hanyar ba da tallafi don yakar cutar.
“Wannan ne ya sanya na zabi wannan rana domin sanar da gudunmawar da zan bayar”, inji shi.
Tsohon gwamnan na Legas ya yaba wa al’ummar jihar bisa matakan kariya daga cutar da suke dauka, kana ya yi kira ga gwamnati da ta himmatu domin ganin bayan annobar.